Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CIKA SHEKARA 90: Tsofaffin Ɗaliban SAS Ta Kano Sun Yi Alƙawarin Raya Makarantar

Shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai Kwalejin koyon harshen Larabci ta Kano (SASOSA) "Class Chapters Forum", Malam Muhammad Abdu, w...




Shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai Kwalejin koyon harshen Larabci ta Kano (SASOSA) "Class Chapters Forum", Malam Muhammad Abdu, wanda ya gama makarantar a 1979, ya bayyana cewa maƙasudin taron cikar Makarantar SAS shekara 90, shi ne haɗa zumunci tsakanin tsofaffin dalibai, tare da alƙawarin ciyar da makarantar gaba.

Da yake zantawa da 'yan jarida a wurin taron, Malam Muhammad ya bayyana cewa an kafa makarantar ne a 1934, daga wannan lokaci zuwa yanzu, shekara 92 ke nan, amma wannan buki da ake yi na shekara 90 ne, domin tun shekaru biyu da suka wuce sun keta shirye-shiryen da za su yi, sai yanzu Allah ya ba da dama.

Ya ce a taron akwai waɗanda suka halarta da suka gama makarantar a 1966, da dan 1958, da kuma wanda a halin yanzu shi ne uba ga tsofaffin ɗalibai, shekararsa 92, Farfesa Galadanci.

Ya ce makarantar ta samar da nasarori masu yawa, domin asalin kafata don a koyar da ilimin addini ne, har zamani ya taso da ita, aka haɗa da ilimin zamani, ko su ma da suka zo bangare biyu suka samu.

Ya ce kamar Farfesa Galadanci, da Limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddin, duk suna raye, kuma suna nan a bangaren addini da na ilimin zamani.

Ya ce duk wanda ya yi wannan makaranta, kamar jefa mutum ne a majalisa, duk inda ya dira daidai ne. To haka suke, 'yan ajinsu sun tafi bangare-bangare, wasu na bangaren mulki, wasu banki, wasu bangaren shari'a, kowane bangare, idan ka je sai ka sami ɗan SAS.

Ya ce sun gode Allah, tsofaffin ɗalibai sun ba da gudumawa don tabbatar da taron. Har ma Gwamnatin Jiha, ba abin da za su ce da Gwamna, sai dai su yi masa addu'a, Allah ya saka masa da alheri, domin in aka duba makarantar yanzu, ba kowace makaranta ta sakandire ce za ka ga kamar ta a halin yanzu ba, yadda aka gyara, sai ka dauka sabon gini ne. Suna yi wa Gwamna addu'ar Allah ya saka masa da alheri.

Ya ce su ɗalibai na wannan makarantar, su san cewa kamar uwa ce a gare su, ta yi musu duk abin da ya kamata na arziki, babu iya kirga irin alkhairin da suka samu dalilin makarantar. Lokaci ya yi da kowane ɗanta, babba da ƙarami, a zo a tattaru a samar da inganci na koyarwa a makarantar.

Ya ce makarantar ba 'yan Kano ne kadai suka more ta ba, duk jahohin Nijeriya ba wacce ba ta da 'ya'yanta a ciki, har ma yanzu akwai dalibai wasu daga Sakkwato, Zariya, Nasarawa, har daga jihohin Igbo.

Ya ce akwai mutane da suka yi makarantar suka yi fice, da ba 'yan asalin Kano ba, wasu sun rasu, kamar Marigayi Grand Khadi na Kaduna da Marigayi Malam Abubakar Gumi. Akwai kuma waɗanda suke a raye, har da Sheikh Ibrahim Zakzaky da Grand Khadi na Gombe, da sauran fitattun mutane da dama da Makarantar SAS suka yi.

Shi ma Daraktan Makarantar ta SAS, Malam Abubakar Idris Gwammaja, ya bayyana mutuƙar farin ciki da bukin cikar makarantar shekaru 90, da ta yaye fitattun mutane a ƙasar nan. Ya ce duk Limaman Babban Masallacin Juma'a na baya da na yanzu, makarantar suka yi.

Ya kuma yaba da irin ƙoƙari da Gwamnatin Jihar Kano take yi ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wajen gyara makarantar. Sannan ya nemi Gwamnati ta ƙara gina musu ɗakunan kwanan ɗalibai, saboda suna da ɗalibai da yawa da suke zuwa daga jihohin faɗin ƙasar nan, da kuma samar musu da masaukin masu hidimar kasa da ake turowa makarantar.

Abubakar Idris Gwammaja, wanda shi ma tsohon ɗalibin makarantar ne, kuma a halin yanzu yake daraktanta, ya yi kira ga dukkan tsofaffin ɗalibai da suka gama makarantar, su ƙara himma wajen ba da gudumuwa, domin bunƙasa ci gaban makarantar mai ɗimbin tarihi.

No comments