Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Barista Muhammad Bello Shehu, ya bai wa masu Ungu...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Barista Muhammad Bello Shehu, ya bai wa masu Unguwanni babura guda 22, tare da Adaidaita Sahu guda biyar da firjuna, ga wasu masu bayar da gudumuwa a tafiyar siyasar sa.
A yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na Social Welfare a Fagge, Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Usman Masu, shi ma ya raba tallafin kuɗi N50,000 ga shugabannin jam'iyyar APC na yankin.
Da yake jawabi a taron, Barista MB Shehu ya ce wannan taron ya shiga tarihi, domin a karo na farko a wannan zango na Dimokuraɗiyya, sun iya tunawa da iyayen ƙasa, waɗanda ba 'yan siyasa ba ne, suka ga dacewar a yi musu wannan tallafi.
Ya ce fatan su, baya ga ɗimbin ayyuka da suke gudanarwa a fannoni daban-daban, kama daga gina makarantu da asibitoci, da aikin hanyoyi da magungunan ruwa, da tallafawa ilimi da bunƙasa ci gaban al'umma, daga yanzu har zuwa bayan zabe, da yardar Allah, za su ci gaba da taba masu Unguwanni da Dagatai da sauran al'ummar da suke wakilta.
Ya ce akwai matasa 'yan gwagwarmaya da aka saba ba su tallafi, kuma bayan wannan taro, taro na gaba na matasa ne.
Hon. Muhammad Bello Shehu ya ce idan aka yi haƙuri, mutane za su amfana da irin waɗannan tallafi, domin ba a taba samun rukunin shugabanni a Ƙaramar Hukumar Fagge ba, da Ɗan Majalisar Tarayya ya yi, na Jiha ya yi, Shugaban Ƙaramar Hukuma ya yi tallafi, da al'umma da aka yi wahala da su irin wannan lokaci ba.
Daga nan ya yi nuni da cewa a baya, kafin su shigo jam'iyyar APC, zai wahala ka ga ana zaune lafiya tsakanin tsohon Ɗan Majalisar Tarayya da Minista na yanzu da Shugaban Ƙaramar Hukuma a Fagge, amma yanzu Allah ya taimaki mutane, aka cire shaiɗanin ciki, yanzu jam'iyyar APC ta zauna lafiya.
Ya ce Allah ya taimake su a Fagge, wani zamani ya zo, duk inda ka shiga an kori siyasar rowa da ta sata da ta karkatar da kuɗin al'umma, kuma duk wanda ya ci yadin mage, lokaci na daf da sai ya yi amansa.
Daga nan MB Shehu ya ja hankalin al'ummar Fagge, da cewa duk wata hayaniya ko rabon kuɗi da babura da Adaidaita Sahu da suke ba, ba zai musu rana ba, idan ranar zabe mutane suka zauna a gida. Ya ce a fito layi, a fito a kwatar wa 'ya'ya da jikokin Ƙaramar Hukumar Fagge yanci.
Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Usman Masu, ya bayyana cewa maƙasudin haɗakar taron shi ne jam'iyyar APC, a matsayinsu na 'ya'yanta, ita ce uwar kowa. Don haka suka kira shugabannin jam'iyya mutum 27 daga kowace mazaba a Ƙaramar Hukumar, sun sauke musu kabakin arziki, suna cewa wannan Dimokuradɗyya da su ake.
Ya ce Ɗan Majalisar Tarayya na Fagge ya bayar da babura 22 da Adaidaita Sahu guda biyar da firji-firji, kuma wannan ba wani abu ne sabo ga Ɗan Majalisar, domin ya bada babura sun fi guda 1000. Shi ya sa kullum in ya sami dama yake cewa MB Shehu ka maimaita, saboda yaro ne mai kirki, mai amfani da damarsa wajen taimaka wa al'umma, suna yi masa fatan ya maimaita.
A ƙarshe, Hon. Salisu Masu ya yi kira ga al'ummar Fagge su fito ranar zabe, maza da mata, su fito su zabi Abba Gida-gida, su zabi APC daga sama har kasa.

No comments