Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jerin Sunayen Janarori 14 Da Suka Yi Ritaya Daga Rundunar Sojojin Nijeriya

Janarori 14 daga rundunar motocin yaƙi masu sulke ta Sojin Ƙasa ta Nijeriya sun yi ritaya daga aikin soja bayan shafe shekaru masu yawa suna...


Janarori 14 daga rundunar motocin yaƙi masu sulke ta Sojin Ƙasa ta Nijeriya sun yi ritaya daga aikin soja bayan shafe shekaru masu yawa suna yi wa ƙasa hidima cikin ƙwarewa da sadaukarwa.

Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a hukumance ranar Asabar.

Sanarwar ta ƙara da cewa an shirya wa manyan hafsoshin soja 14 bikin bankwana na musamman a ranar Asabar, domin karrama su bisa irin jajircewa, sadaukarwa da gagarumar gudummawar da suka bayar ga rundunar sojin ƙasar da kuma Nijeriya baki ɗaya.

Ga jerin hafsoshin da aka karrama:

* Laftanar Janar AB Ibrahim

* Manjo Janar MS Ahmed

* Manjo Janar OC Ajunwa

* Manjo Janar JO Ochai

* Manjo Janar IS Ali

* Manjo Janar SG Muhammed

* Manjo Janar IM Jallo

* Birgediya Janar S Ahmadu

* Birgediya Janar VO Ita

* Birgediya Janar UM Aliyu

* Birgediya Janar AG Nura

* Birgediya Janar T Isa

* Birgediya Janar EB Barkins

* Birgediya Janar AM Usman

Jaridar Herald Sun ta ruwaito cewa an gudanar da bikin bankwanar ne a filin fareti na Birgediya Janar Y. Abubakar, da ke barikin sojoji na Obienu, a Bauchi.

Bikin bankwana irin wannan wata dadaddiyar al’ada ce a rundunar soja, wadda ke nuna girmamawa da jinjinawa ga hafsoshin da suka yi ritaya, tare da nuna godiya a hukumance bisa hidimar da suka yi. Haka kuma, bikin na zama wata dama ta tunawa da nasarorin da suka samu da kuma gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa rundunar motocin yaƙi masu sulke ta Sojin Ƙasa da inganta ayyukanta na yaƙi.

No comments