Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da duk wasu ayyuka na Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, tare da kafa wani ƙwaƙƙwaran kwamitin bincik...
Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da duk wasu ayyuka na Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, tare da kafa wani ƙwaƙƙwaran kwamitin bincike bisa zargin cin zarafin wata Baturiya 'yar yawon buɗe ido.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Katsina, Bala Salisu Zango ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, 24 ga Nuwamba, 2026.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta nuna matuƙar damuwarta bisa zargin da ake yaɗawa, inda ta bayyana cewa tana ɗaukar lamarin da muhimmanci.
Kwamishin yaɗa labaran ya ƙara da cewa, bGwamna Dikko Umaru Radda ya kuma bayar da umarnin kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan lamarin, tare da gabatar wa gwamnati da sakamakon bincikensa da shawarwarin matakan da ya kamata a ɗauka.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta dakatar da dukkan ayyukan Sarkin Daura, ciki har da tafiye-tafiyensa da suka shafi harkokin masarautar.
Gwamnatin ta tabbatar wa al’umma cewa za a tabbatar da adalci, tare da aiwatar da shawarwarin da kwamitin binciken zai gabatar.
Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Ya zuwa kammala wannan rahoto, gwamnatin ba ta bayyana sunaye shugaba da mambobin wannan kwamitin ba, ko wa’adin da aka ba su na kammala binciken.

No comments