Gwamnatin Jihar Kaduna ta jajanta wa mahukunta da ma'aikatan gidan rediyon tarayya na Kaduna (FRCN) bisa Ifti'lain gobarar da ta tas...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta jajanta wa mahukunta da ma'aikatan gidan rediyon tarayya na Kaduna (FRCN) bisa Ifti'lain gobarar da ta tashi a gidan rediyon, tare da alƙawarin duba hanyoyin tallafa wa gidan.
Kwamishinan Ma'aikatar YaÉ—a Labarai da Al'adu ta Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci manyan jami'an ma'aikatar ziyarar gani da ido a gidan rediyon domin duba irin barnar da gobarar ta yi.
A yayin ziyarar, an zagaya da Ƙwamishinan zuwa sassa da wuraren da gobarar ta shafa domin ya gani da idonsa irin barnar da ta haddasa, da kuma fahimtar halin da gidan rediyon ke ciki sakamakon iftila'in.
Maiyaki ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin, gwamnatin jihar ta tura jami'an hukumar kashe gobara domin bayar da agajin gaggawa da kuma shawo kan gobarar.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta duba hanyoyin da za ta tallafa wa gidan rediyon, musamman ganin yadda al'ummar jihar Kaduna ke amfana da shirye-shiryensa, kasancewar gidan rediyon na daya daga cikin manyan kafafen yada labarai da ke jihar.
Kwamishinan ya kuma yi addu'ar Allah ya kare afkuwar irin wannan iftila'i a nan gaba.
A nasa jawabin, Shugaban shiyya na gidan rediyon , Malam Aminu Abdullahi Gombi, ya nuna godiya da jin dadinsa bisa yadda gwamnatin jihar ta nuna damuwa tare da É—aukar matakin kai ziyara tun bayan faruwar gobarar.
Ya kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta tallafa wa gidan rediyon wajen tallata ayyukanta da shirye-shiryenta, domin ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin kafar yaɗa labaran da gwamnati.


No comments