Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, murnar cika sh...
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, murnar cika shekaru 45 da haihuwa.
Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, cewa Tinubu ya bayyana Bichi, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Bichi a Jihar Kano, a matsayin ɗan majalisa mai ƙwazo, basira da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukan majalisa da ci gaban ƙasa.
Shugaban Ƙasar ya yaba da rawar da Bichi ke takawa a matsayinsa na shugaban ɗaya daga cikin muhimman kwamitocin Majalisar Wakilai, musamman wajen jagorantar nazari da tantancewa da kuma amincewa da kasafin kuɗin ƙasa na shekara-shekara. Ya kuma yaba da wakilcin da yake yi wa al’ummarsa da ayyukan da ya ce sun shafi ilimi, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa matasa.
Bola Tinubu ya kuma bayyana cewa Bichi ya bambanta kansa tun bayan zaɓensa na farko zuwa Majalisar Wakilai a shekarar 2019, inda ya taɓa jagorantar Kwamitin Ayyuka a Majalisa ta Tara, kafin ya zama Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi a Majalisa ta Goma. Ya roƙe shi da ya ƙara mayar da hankali wajen yi wa al’ummarsa da ƙasa hidima, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, hikima da ƙarfi.

No comments