Daga Zubairu Lawal, Lafia Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ƙaddamar da tituna uku masu tsawon kilomita 4.4 da kuma kasuwar zamani ...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ƙaddamar da tituna uku masu tsawon kilomita 4.4 da kuma kasuwar zamani a Ƙaramar Hukumar Doma ta jihar.
Da yake jawabi a wajen taron a Doma, Gwamna Sule ya ce ƙaddamar da ayyukan na daga cikin shirye-shiryen bikin cika shekaru 30 da kafuwar Jihar Nasarawa.
Ya sanar da cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida na jihar (IGR) sun ƙaru daga Naira biliyan 7 a duk shekara a shekarar 2019 zuwa kusan Naira biliyan 40 a yanzu, lamarin da ya bai wa gwamnati damar aiwatar da manyan ayyuka ba tare da karɓar bashi ba.
Ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da titin kilomita 1.7 daga RCM Primary School Junction zuwa Yelwa Garage, tare da hanyar haɗi zuwa Fadar Andoma; titin kilomita 2.7 daga Timber Shade zuwa GSS Odorogya zuwa St. Aloysius Road, da kuma Kasuwar Zamani ta Doma.
Sule ya ce an kashe sama da Naira biliyan 2 daga cikin Naira biliyan 3 na kuɗin tallafin gwamnatin tarayya domin magance ambaliyar ruwa, tare da ƙarin kuɗaɗen shiga na cikin gida na jihar, wajen gina muhimmiyar gada da ta haɗa Lafia da Doma domin magance matsalar ambaliyar ruwa da ke faruwa akai-akai.
Ya ce, “Mun tara kuɗaɗe masu yawa. Da kuɗaɗen da muka tara, mun aiwatar da ayyuka domin jama’a, saboda manufar gwamnati ita ce yi wa jama’a hidima.
“Shin za ku zaɓi wanda yake cewa, ‘zan yi kaza da kaza’, ko kuma wanda yake cewa, ‘na yi kaza da kaza’?” in ji shi.
Gwamnan ya kuma lissafa ayyukan filayen wasa da ake ci gaba da ginawa a Doma, Toto, Wamba, Garaku da ke Ƙaramar Hukumar Kokona, Keffi da Akwanga, inda ya ce za a kammala filin wasan Doma zuwa watan Nuwamba.
Ya yi alkawarin dawowa domin ƙaddamar da wasu ayyukan, tare da ba da fifiko wajen gina hanyar Doma-Rukubi-Akpanaja.
Ya ce Doma ta samu gagarumar fa’ida a ƙarƙashin gwamnatinsa, inda ya bayyana cewa an samu Kwamishinoni biyu, Sakatarorin dindindin huɗu da kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnati ɗaya daga yankin.
Gwamnan ya kuma buƙaci al’ummar yankin su nuna godiya a zaɓe mai zuwa.
Tun da farko, Manajan Darakta na Hukumar Raya Birane ta Jihar Nasarawa, Mohammed Wada-Yahaya, ya ce titunan da aka ƙaddamar sun cika ƙa’idojin kwangilar.
Ya ce, “Dukkan titunan suna da magudanan ruwa, kuma an gina su bisa ƙa’idar Standard Type 1, tare da shimfiɗa kwalta da magudanan ruwa na ƙarfafan siminti.”
Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Doma, Jonathan Addra, ya bayyana ranar a matsayin tarihi, inda ya ce tun daga shekarar 1999 ba a taɓa ƙaddamar da manyan ayyuka uku a rana guda a Doma ba.
Ya gode wa Sule bisa amincewa da gina ƙaramin filin wasa, sannan ya jero wasu ayyukan majalisar ƙaramar hukumar, ciki har da ginin wurin aiki a Akpanaja da asibitin maganin cizon maciji domin manoma.
Ya buƙaci a mayar da Aroma-Yaa-Alarama Road zuwa titin kwalta, tare da gina hanyar Doma-Agbashi-Akpanaja.
Shi ma Andoman Doma, Alhaji Ahmadu Aliyu Ogah-Onawo, ya yaba wa Gwamna Sule bisa buɗaɗɗen shugabanci da kuma kyakkyawan tsarin kula da albarkatun gwamnati.
Ya ce, “Kai ne mutum ɗaya tilo da kullum kake bayyana abin da ka yi da albarkatun da aka ba ka. Ba ka bar mu cikin shakku game da inda ka sanya kowace irin hanya ta albarkatu ba.”
Ya yaba wa Gwamnan bisa jawo masu zuba jari a fannonin noma da ma’adinai, yana mai cewa ma’adinan da ke Jihar Nasarawa na daga cikin mafi inganci a duniya.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ƙara wa gwamnatin jihar albarkatu domin ta samu damar kawo ci gaba ga dukkan ƙananan hukumomi 13 na jihar.

No comments