Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JIHAR NASARAWA @30: Gwamna Sule Ya Nemi Al'umma Su Ci Gaba Da Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

Daga Zubairu Lawal, Lafia Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da tabbatar da haɗin kai da zam...


Daga Zubairu Lawal, Lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya, yana mai cewa waɗannan su ne ginshiƙan ci gaba da kuma jawo masu zuba jari zuwa jihar.

Sule ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Lafia, yayin bikin Nasarawa Carnival, wanda aka shirya a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 30 da ƙirƙirar Jihar Nasarawa.

Gwamnan ya gode wa mahalarta taron, ƙungiyoyin al’adu da manyan baki, ciki har da Shugaban Global Alliance da ya zo daga Ireland, Shugaban Nigerian Institute of Public Relations (NIPR), Darakta-Janar na Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido ta Ƙasa, da wakilia dabam- dabam a Jihar, bisa yadda suka nuna kyawawan al’adu da tarihin jihar.

Ya ce, “Haƙiƙa Jihar Nasarawa ta kai matsayin balaga. Daga abin da muka gani, kun nuna cewa har yanzu mu al’umma ce da ke alfahari da al’adunmu.”

Gwamna Sule ya ce bikin Carnival na daga cikin shirye-shiryen da aka tsara domin bikin cika shekaru 30 da kafuwar jihar, inda ya ƙara da cewa za a gudanar da taron tattaunawa kan yadda aka ƙirƙiri jihar da kuma makomarta ta fuskar ci gaba, tare da wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunta tsakanin jihohin Nasarawa da Plateau.

Ya bayyana cewa an ƙirƙiri Jihar Nasarawa ne daga tsohuwar Jihar Plateau, inda ya yaba wa Gwamnan Jihar Plateau da zai jagoranci tawagarsa, da tsohon Gwamna Simon Bako Lalong da tsohuwar Mataimakiyar Gwamna Pauline Tallen, bisa amsa gayyatar da aka yi musu.

Sule ya kuma yaba wa waɗanda suka ƙera motar Solid Minerals Truck, wadda ta nuna albarkatun ma’adinan jihar, yana mai cewa Nasarawa na da dukkan ma’adinai bakwai masu muhimmanci da ake samu a Najeriya.

Ya ce jihar ta yi amfani da wannan baiwar da Allah Ya hore mata wajen jawo masu zuba jari, waɗanda ba kawai suke hako ma’adinan ba, har ma suna sarrafa su a cikin jihar, ciki har da babbar masana’antar sarrafa lithium mafi girma a Afirka.

Ya ce, “Dukkan waɗannan abubuwa suna faruwa ne saboda yadda muke rayuwa tare a matsayin al’umma.”

Dangane da siyasa, gwamnan ya yi kira ga ‘yan siyasa da su riƙa yin sabani cikin mutunta juna yayin da zaɓe ke ƙaratowa, yana mai cewa iko yana hannun Allah Maɗaukakin Sarki ne.

Ya ce, “Zaɓe na zuwa nan ba da jimawa ba. Na san ba za mu kasance da ra’ayi ɗaya ba, amma mu yi sabani cikin mutunta juna. Mu gudanar da dimokuraɗiyya yadda ya kamata.”

Ya ƙara da cewa, “Kada ku saurari duk wanda ke da sha’awar haifar da rashin jituwa a tsakaninmu saboda siyasa.

 Za mu iya yin sabani mu cimma matsaya, kuma za mu iya cimma matsaya mu yi sabani. Ba batun rai da mutuwa ba ne.”

Gwamna Sule ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin tarayya ta aiwatar, yana cewa sauye-sauyen suna bai wa jihohi damar samar da nasu wutar lantarki, ƙara samun kuɗaɗen shiga da kuma inganta tsaro.

Ya bayyana cewa Jihar Nasarawa ta karɓi kudirin dokar kafa ’yan sandan jiha, kuma jihar za ta mara wa kafa su baya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a jihar.

Ya yi gargaɗin cewa, “Yawancin masu zuba jari da ke kallon Nasarawa za su ci gaba da kallon Nasarawa ne kawai idan akwai zaman lafiya a Nasarawa.”

Nasarorin gwamnatin Sule
Da yake waiwayen mulkinsa tun daga shekarar 2019, Sule ya ce gwamnatinsa ta inganta zaman lafiya, jin daɗin ma’aikata, kiwon lafiya da ilimi a jihar.

Ya kuma bayyana farin cikinsa da halartar Cibiyar Koyar da Sana’o’i da Fasaha a bikin, yana mai cewa mayar da hankali kan sana’o’i ya yi daidai da akidar gwamnatinsa ta koyar da dabarun sana’a domin dogaro da kai.

Gwamna Sule ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 30, tare da addu’ar cewa a cikin shekaru 30 masu zuwa, jihar za ta samu ci gaba da sauye-sauye fiye da yadda ake gani a yanzu.

Ya ƙara da cewa, “Idan mutum yana nan shekaru 30 da suka gabata kuma ya zo Lafia a yau, ba zai gane cewa wannan ita ce Lafia ɗin ba. Wannan shi ne aikin haɗin kai. Wannan shi ne aikin shugabanci. Kuma wannan shi ne abin da ya kamata mu ci gaba da yi.”
 

No comments