Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

’Yan Sanda Sun Cafke Ɗan Bindiga Yana Cire Kuɗin Fansa A POS

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta cafke wani mutum mai suna Muhamodu Sanni, wanda ake zargi da kasancewa ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar...




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta cafke wani mutum mai suna Muhamodu Sanni, wanda ake zargi da kasancewa ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar masu garkuwa da mutane, yayin da yake ƙoƙarin cire kuɗin fansa a wani mashin ɗin POS a ƙaramar hukumar Ilorin ta Gabas.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ta ce an kama wanda ake zargin ne sakamakon wani aikin bincike da aka gudanar bisa bayanan sirri.

Ta ce binciken ya biyo bayan sace wasu mutane uku da aka yi a ranar 28 ga Yuli, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari kauyen Obudu.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun faɗaɗa binciken nasu tare da bibiyar hanyoyin sadarwa da kuma mu’amalar kuɗaɗen da ake zargin ƙungiyar masu garkuwa da mutanen na amfani da su. Wannan ne ya taimaka wajen gano inda Sanni yake, har aka yi nasarar cafke shi.

A cewar Ejire-Adeyemi, wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu wajen karɓo kuɗaɗen fansa, sannan ya bai wa jami’an tsaro bayanan wasu mutane biyu da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar, waɗanda ta bayyana sunayensu da Aminu da Umar.

Rundunar ta ce bayanan da aka samu daga Sanni sun samar da wasu sabbin hanyoyin da za su taimaka wajen zurfafa binciken da kuma gano sauran mutanen da ke da hannu a ayyukan ƙungiyar.

Kakakin rundunar ta bayyana nasarar cafke wanda ake zargin a matsayin wani ci gaba da ke nuna muhimmancin dabarun tsaron da ya dogara da tattara bayanan sirri, wanda Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ke ƙarfafawa.

Shi ma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ojo Adekimi, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka a jihar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro ingantattun bayanai game da ayyukan masu laifi, domin hakan zai taimaka wajen hana aikata laifuka da kuma cafke waɗanda ke da hannu a cikinsu.

No comments