Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Satar Babura Sun Kashe ’Yan Acaba 10 Cikin Watanni Biyu A Nasarawa

Shugaban reshen Ƙungiyar ’Yan Acaba na Lafia, Uba Yahaya, ya bayyana cewa a cikin watanni biyu da suka gabata, an kashe aƙalla ’yan acaba 10...



Shugaban reshen Ƙungiyar ’Yan Acaba na Lafia, Uba Yahaya, ya bayyana cewa a cikin watanni biyu da suka gabata, an kashe aƙalla ’yan acaba 10 a babban birnin Jihar Nasarawa, Lafia.

Yahaya ya bayyana hakan ne yayin da yake yin Allah-wadai da yadda hare-haren da ake kai wa ’yan ƙungiyar ke ƙara ta’azzara, yana mai cewa wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga ne ke kai musu hare-haren da nufin kwace baburansu.

Ya ce lamarin ya jefa ’yan okada a Lafia cikin fargaba, musamman yayin da suke fita neman abin da za su ci domin tallafa wa iyalansu.

Shugaban ƙungiyar ya ce ya shaida irin mummunan tasirin hare-haren da ake kai wa mambobinsu, inda ya bayyana cewa shi da kansa ya halarci jana’izar dukkan ’yan acaba 10 da aka kashe.

“Mu da kanmu mun halarci jana’izar mutane 10,” inji Yahaya.

Ya ce waɗannan ba alkaluma kawai ba ne, illa dai mutane ne daga cikinsu da aka kashe cikin zalunci yayin da suke neman na abinci.

Yahaya ya bayyana cewa an kwace dukkan baburan mutanen da aka kashe, yana mai cewa wasu daga cikin hare-haren na faruwa ne cikin mummunan yanayi.

Ya kawo misalin wani ɗan okada da aka daddatsa da wani abu mai nauyi a kan hanyar kewaye da birnin, yayin da a wani hari kuma aka daba wa wani ɗan okada wuka kai tsaye a zuciya tare da fasa masa kai.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka kai wa hare-haren sun tsira da raunuka, amma masu laifin suka tafi da baburansu.

Shugaban ƙungiyar ya ce yanayin tsaro a yankin ya sake tabarbarewa, duk da cewa matakan tsaro da gwamnatin jihar ta ɗauka a baya sun ɗan kawo sauƙi.

A cewarsa, nasarar da aka samu a wancan lokaci ta sa wasu ’yan okada da jami’an tsaro suka sassauta taka-tsantsan, abin da ya bai wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka damar sake haɗuwa tare da dawo da hare-haren cikin tsanani.

Yahaya ya ce mafi yawan hare-haren na faruwa ne da yamma tsakanin lokacin Sallar Magariba da Isha’i, ko da yake har yanzu ana samun hare-hare da rana.

Ya ce masu aikata laifukan sun ƙware wajen amfani da dabarun yaudara domin jawo ’yan acaba zuwa wuraren da ba kowa.

A wasu lokuta, masu laifin kan yi kamar matafiya da suka makale ko kuma masu gyaran babura, domin samun damar jan hankalin ɗan okada ya kai su inda za su iya kai masa hari.

Abin da ya fi tayar da hankali, a cewar Yahaya, shi ne yadda wasu daga cikin masu fashin baburan ke amfani da rigunan aikin ’yan acaba da gwamnati ta raba, domin su ɓoye ainihin su tare da yaudarar waɗanda suke kai wa hari.

Ya bayar da misalin wani matashi da aka yi wa fashin babur kwanan nan, inda ya ce masu laifin sun sanya irin waɗannan riguna, abin da ya sa matashin bai yi zargin komai ba har sai da suka yi amfani da amincewar da yake da ita wajen kai masa hari tare da kwace baburinsa.

No comments