Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babbar Hanyar Sokoto-Badagry Mai Tsawon Kilomita 1000 Za Ta Bunkasa Noma A Arewa – Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,000 zai ta...

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,000 zai taimaka wajen bunƙasa noma da buɗe sabbin damar tattalin arziki ga al’ummomi da jihohin da hanyar za ta ratsa, ciki har da Jihar Kebbi.

Idris ya bayyana haka ne a Abuja, lokacin da tawagar masu yaɗa labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Yakubu Birnin-Kebbi, ta kai masa ziyarar ban girma. Ya ce kusan kilomita 250 daga cikin hanyar za su ratsa Kebbi, lamarin da zai bai wa jihar damar ƙara faɗaɗa harkokin noma, kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziki.

Ministan ya ce aikin ba wai hanya ce kawai ta haɗa garuruwa da jihohi ba, domin ana sa ran samar da madatsun ruwa kusan 63 a kan layin hanyar, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa noma, samar da wutar lantarki da sauran ayyukan tattalin arziki. Ya kuma yaba wa Gwamnatin Kebbi kan haɗin gwiwar da take yi da Gwamnatin Tarayya a fannonin noma, ababen more rayuwa da tsaro.

Ya ce irin waɗannan manyan ayyukan more rayuwa na daga cikin ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kai ci gaba kusa da jama’a, tare da samar da yanayin da zai bai wa ‘yan kasuwa da al’umma damar bunƙasa. A cewarsa, yawancin al’ummar Najeriya suna zaune ne a jihohi, ba Abuja ba, don haka ya zama wajibi a kai ci gaba inda jama’a suke.

A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kebbi ya ce tawagar ta je Abuja ne domin gabatar wa ministan bayanai kan nasarorin da gwamnatin jihar ta samu tare da ƙarfafa alaƙarta da Gwamnatin Tarayya. Ya ce Kebbi na da babbar dama a fannonin noma, ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da tsaro, kuma jihar na ƙudurin ci gaba da haɗa hannu da Gwamnatin Tarayya domin amfani da wannan damar wajen bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

 

No comments