Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekaru 29, Abubakar Musa, bisa zargin yunƙurin amfani da kwafin Alƙur’ani da wasu a...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekaru 29, Abubakar Musa, bisa zargin yunƙurin amfani da kwafin Alƙur’ani da wasu abubuwa wajen wani tsafi da ake zargin an shirya domin sanya wata budurwa ta zama mai biyayya gare shi fiye da kima.
Musa, ɗan ƙauyen Rafin Mose da ke Ƙaramar Hukumar Zuru, na fuskantar zarge-zargen haɗa baki wajen aikata laifi, wulaƙanta littafin addini, amfani da tsafi da sihiri, da kuma tunzura al’umma da ka iya haifar da rikici.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 9 ga Agusta 2026, da misalin ƙarfe 7 na dare, a yankin Zango da ke Zuru.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar ranar Juma’a, rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa Musa ya yi aiki tare da wasu mutane biyu da ake zargi, wato Rabi’u Tela, mijin Zarau Hassan, da kuma Hamza Zango.
A cewar ’yan sandan, mutanen biyu sun tsere kuma ana ci gaba da neman su.
Usman ya ce waɗanda ake zargin sun haƙa wani rami a cikin ɗakin Zarau Hassan, inda suka binne kwafin Alƙur’ani mai girma tare da wasu abubuwa da suka haɗa da maniyyi, goro fari da ja, kayan ɗaki, gawawwakin dabbobi da wasu kayayyakin da rundunar ta bayyana a matsayin kayan tsafi.
’Yan sandan sun ce an yi zargin wannan abu ne da nufin sanya Hassan ta zama mai biyayya ga mijinta, Tela.
Rundunar ta bayyana cewa yanayin wannan zargin na iya tayar da hankalin Musulmi a yankin tare da haifar da ɓarkewar zaman lafiya.
A halin yanzu, Musa na tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran mutane biyun da ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta ce za a gurfanar da Musa a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai gargadin cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukar matakin da doka ta tanada kan duk wanda ayyukansa suka yi barazana ga zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, oda da zaman lafiya a cikin al’umma.
Rundunar ta kuma buƙaci mazauna jihar da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro.
Ta tabbatar wa jama’a cewa za a kiyaye sirrin duk bayanan da aka bayar domin taimakawa wajen gano masu aikata laifuka da kuma kare zaman lafiyar al’umma.
.jpeg)
No comments