Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fuskanci suka bayan da ya kira Birtaniya da sunan ‘Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya’, yayin d...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fuskanci suka bayan da ya kira Birtaniya da sunan ‘Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya’, yayin da yake sukar sauyin matsayar ƙasar kan Isra’ila da rikicin Gabas ta Tsakiya.
Netanyahu ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da shirin Melech Blitzer Haim, wani faifan tattaunawa na yanar gizo a Isra’ila, wanda aka watsa ranar Alhamis.
A yayin hirar, firaministan na Isra’ila yana magana ne kan yadda kafafen yaɗa labarai na Birtaniya ke ɗaukar rahotannin da suka shafi Isra’ila.
Ya yaba wa marubucin Birtaniya, Randolph Churchill, kan irin rahotannin da ya rubuta lokacin yaƙin kwanaki shida na shekarar 1967.
Sai dai Netanyahu ya bambanta wannan da abin da ya ce shi ne yadda kafafen yaɗa labaran Birtaniya ke gudanar da rahotonsu a yanzu.
Netanyahu ya yi amfani da kalmar ne cikin yanayin habaici, inda ya kira Birtaniya da “Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya”, kafin ya danganta batun da shirin nukiliyar Iran.
Ya ce, “Wani ya ce jamhuriyar Musulunci ta farko da za ta mallaki makaman nukiliya za ta kasance Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya. Muna tabbatar da cewa ba za a samu wata irin wannan a Iran ba.”
Da aka tambaye shi ko yana ganin wannan bayanin ya shafi Turai baki ɗaya, Netanyahu ya amsa da cewa: “Eh.”
Furucin Netanyahu ya jawo suka daga wasu fitattun Yahudawa da tsoffin jami’an Birtaniya, waɗanda suka ce kalaman na iya ƙara rura wutar ƙiyayya ko wariya ga Musulmi.
Gavin Barwell, wanda ya taɓa zama shugaban ma’aikatan ofishin Firaministan Birtaniya a zamanin tsohuwar Firaminista Theresa May, ya bayyana kalaman a matsayin na kyamar Musulunci.
Barwell ya rubuta a shafin X cewa lokaci ya yi da mutane za su daina ɗaukar Netanyahu a matsayin abokin Birtaniya.
Haka kuma, Rabbi Charley Baginsky da Rabbi Josh Lev, waɗanda ke jagorantar Movement for Progressive Judaism, sun soki kalaman firaministan na Isra’ila.
Sun ce kalaman sun fi tayar da hankali ne a daidai lokacin da Birtaniya ke fama da damuwar ƙiyayya ga Yahudawa, ƙiyayya ga Musulmi da kuma ƙaruwar rikice-rikicen zamantakewa.
Sun jaddada cewa, “Firaminista Netanyahu ba ya magana a madadin Yahudawan Birtaniya. Kalamansa ba sa wakiltar mu.”
Kalaman Netanyahu sun zo ne a daidai lokacin da dangantakar Isra’ila da Birtaniya ke ƙara samun tsaiko sakamakon yakin Gaza da kuma rikicin Isra’ila da Falasɗinawa.
Gwamnatin Birtaniya ta sha sukar ayyukan sojin Isra’ila a Gaza, tare da dakatar da wasu lasisin fitar da makamai zuwa Isra’ila.
Birtaniya ta kuma kakabawa wasu ministocin gwamnatin Isra’ila masu tsattsauran ra’ayi, Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, takunkumi.
Bugu da ƙari, London ta ƙara nuna goyon baya ga batun kafa ƙasar Falasɗinu tare da yin suka kan wasu manufofin Isra’ila a yankunan Falasɗinawa da Isra’ila ta mamaye.
Wannan matsaya ta ƙara zurfafa rashin jituwar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu, duk da dadaddiyar alaƙarsu ta siyasa da tsaro.
Maganar Netanyahu game da Birtaniya ta kasance wani ɓangare na babban muhawararsa kan shirin nukiliyar Iran.
Firaministan Isra’ila ya dade yana bayyana shirin nukiliyar Iran a matsayin babbar barazana ga tsaron Isra’ila, yana mai cewa bai kamata Tehran ta samu damar mallakar makaman nukiliya ba.
Saboda haka, haɗa kalmar “Jamhuriyar Musulunci” da Birtaniya, sannan nan take ya koma kan Iran, na nuna cewa Netanyahu yana amfani da kwatancen ne wajen sukar abin da yake gani a matsayin matsayar Birtaniya da wasu ƙasashen Turai da ke ƙara sukar manufofin Isra’ila.
Ana sa ran wannan sabon rikici zai ƙara dagula dangantakar Landan da Jerusalem, musamman yayin da ƙasashen Yammacin duniya ke fuskantar matsin lamba kan yadda za su mayar da martani ga ayyukan Isra’ila a Gaza, tare da tunkarar sauran rikice-rikicen da suka shafi Iran.

No comments