Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ya Sake Buɗe Damar Gwajin Sabbin Fasahohin Hadahadar Kuɗi Da Kadarorin Zamani

Daga Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa ya buɗe kashi na biyu na Shirin Gwajin Sabbin Dokokin Fasahohin Kuɗ...

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa ya buɗe kashi na biyu na Shirin Gwajin Sabbin Dokokin Fasahohin Kuɗi, inda ya samar da hanyoyin gwaji na musamman ga sabbin fasahohin da suka shafi kadarorin zamani da kuma ayyukan kuɗi da ke amfani da bayanai.

Matakin na CBN na nufin daidaita bunƙasar fasahar hadahadar kuɗi da tabbatar da zaman lafiyar tsarin kuɗi da kuma kare masu amfani da ayyukan kuɗi.

A ƙarƙashin wannan sabon rukuni na biyu na tsarin, masu ƙirƙirar fasaha da suka cancanta, cibiyoyin kuɗi, masu samar da ayyukan kadarorin zamani, kamfanonin fintech da kamfanonin fasaha za su samu damar gwada sabbin kayayyaki, ayyuka, tsarin kasuwanci da fasahohin tallafi a cikin wani yanayi wanda CBN ke sa ido a kai.

CBN ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktar Riƙo a Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari, Hajiya Hakama Sidi Ali ta fitar a Abuja.

Ta ce shirin zai taimaka wajen tsara dokoki yayin da tsarin hada-hadar kuɗi na zamani ke ci gaba da sauyawa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon tsarin manyan hanyoyin biyan kuɗi na Nijeriya ya bayyana cewa ya sarrafa hada-hadar kuɗi har sau miliyan 26.55 da darajar su ta kai Naira tiriliyan 1.4, tsakanin cibiyoyi 48 da ke cikin tsarin, kimanin shekara guda bayan da tsarin 'Nigeria Inter-Bank Settlement System' (NIBSS) Plc ya ƙaddamar da shi.

Ana sa ran wannan shirin zai samar da ingantacciyar hanyar da za ta bayar da damar gwada sabbin fasahohin kuɗi a yanayi na zahiri ba tare da fallasa tsarin kuɗin ƙasa ga haɗurran da ba a sarrafa su ba.

CBN ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin sa na gina tsarin kuɗi mai ƙirƙira, juriya da kuma haɗa kowa da kowa, wanda zai taimaka wajen samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa tare da kiyaye aminci, inganci da mutuncin tsarin kuɗin Nijeriya.

Wannan rukuni na biyu na shirin ya ƙunshi hanyoyin gwaji guda biyu na musamman: 'VASP Track da Data-Enabled Financial Services (Non-VASP) Track'.

Tsarin VASP Track zai mayar da hankali kan sabbin abubuwan da suka shafi kadarorin zamani, biyan kuɗi, kammala hadahadar kuɗi, adana kadarori, asusun 'wallets' da sauran abubuwan more rayuwa na kuɗi da ke buƙatar gwaji kai-tsaye ƙarƙashin kulawar hukumomi.

A gefe guda kuma, shi 'Data-Enabled Financial Services Track' zai mayar da hankali kan sabbin abubuwan da ke amfani da ingantattun hanyoyin dijital da raba bayanai bisa izini domin inganta hadahadar kuɗi, biyan kuɗi, lamuni, sarrafa ƙalubale, ingancin ayyuka da kuma kyautata sakamakon da masu amfani ke samu.

A cewar Hajiya Hakama, an tsara shirin ne domin bai wa masu ƙirƙira da masu kula da harkokin kuɗi damar yin hulɗa a duk tsawon lokacin gwajin, ta yadda ɓangarorin biyu za su koya daga yadda ake amfani da sabbin fasahohin a aikace.

Ta ce wannan tsari zai taimaka wajen fahimtar abubuwan da suka shafi dokoki tare da ƙarfafa sabbin fasahohin da za su samar da fa'ida ga masu amfani da kuma tsarin kuɗin ƙasa baki ɗaya.

Shi ma Daraktan Sashen Manufofin Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Musa Jimoh, ya ce sabbin fasahohin kuɗi na ci gaba da sauya yadda mutane da kamfanoni ke samun damar amfani da ayyukan kuɗi.

Ya ce tsarin wanda a Turance ake kira 'Regulatory Sandbox' na CBN, wanda aka samar ta hanyar fasaha tare da haɗin gwiwar EMTECH, yana ba masu ƙirƙira da masu tsara dokoki damar yin aiki tare cikin tsari, domin gwada sabbin hanyoyin da ke da alƙawari cikin kulawa tare da samar da kariya ga masu amfani da tsarin kuɗi.

Ya ƙara da cewa ƙaddamar da hanyoyin gwaji na musamman ga 'VASPs' da ayyukan kuɗi da ke amfani da bayanai na nuna sauyin yanayin sabbin fasahohin kuɗi da kuma ƙudurin CBN na tabbatar da cewa dokokin Nijeriya suna ci gaba da tallafa wa sabbin fasahohi masu inganci, gaskiya da kuma daidaita su da dogon burin ci gaban tsarin kuɗin ƙasar.

CBN ya ce ƙaddamar da rukuni na biyu ya yi daidai da ƙudurin sa na samar da yanayin dokoki mai gaskiya, daidaitacce kuma bisa la'akari da haɗari, wanda ke ƙarfafa ƙirƙira ba tare da yin illa ga daidaiton kuɗi da tsarin tattalin arziki ba.

CBN ta ƙara da cewa darussan da za a samu daga gwaje-gwajen da ake gudanarwa ƙarƙashin kulawa za su taimaka wajen ƙara fahimtar sabbin fasahohi da kuma tsara dokoki da tsarin sa-ido da za su dace da sauyin yanayin tsarin kuɗi na dijital.

A ƙarƙashin shirin, ba za a amince da mai nema kawai saboda yana da sabuwar fasaha ko tsarin kasuwanci ba.

Maimakon haka, CBN za shi tantance aikace-aikacen bisa wasu ƙa'idoji, ciki har da matakin ƙirƙira, shirye-shiryen gudanar da gwaji kai tsaye cikin yanayi mai kulawa, fa'idar da za a iya samu ga masu amfani ko kasuwa, tsarin shugabanci, ƙarfin sarrafa haɗari da kuma dacewar tsarin gwajin da aka gabatar.

Masu neman da suka yi nasara za su gudanar da gwaje-gwaje ƙarƙashin kulawa cikin iyakokin da CBN ta amince da su.

Tsarin gwajin zai ƙunshi matakan kariya da suka shafi kare masu amfani, juriyar ayyuka, tsaron yanar gizo da kuma bayar da rahotannin da hukumomi suka tanada, lamarin da ke nuna muhimmancin da CBN ke bai wa tabbatar da cewa ƙirƙira ba ta zuwa da illa ga mutuncin tsarin kuɗi.

Wannan tsari na da muhimmanci musamman ga sabbin kamfanonin kadarorin zamani, waɗanda ke aiki a wani fanni da bunƙasar fasaha kan zarce tsarin dokokin gargajiya cikin sauri.


Sai dai CBN ya fayyace cewa shiga cikin tsarin ba yana nufin an ba kamfani lasisin gudanar da ayyukan kuɗi ba.


Ya ce shiga cikin shirin ba lasisi, izini ko amincewa ba ne na gudanar da ayyuka a wajen iyakokin gwajin da CBN ta amince da su.

Maimakon haka, an tsara shi ne domin sauƙaƙa gwaje-gwaje cikin kulawa, ƙarfafa hulɗa tsakanin masu ƙirƙira da masu tsara dokoki, da kuma samar da bayanan da za su taimaka wajen tsara manufofi da dokokin nan gaba.

Za a fara aikace-aikacen shiga rukuni na biyu na shirin daga 12 zuwa 31 ga Agusta, 2026.
 

No comments