Ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Rt. Hon. Isa Mohammed Ashiru Kudan (Sarkin Bai Zazzau), ya amince da naɗin wasu ...
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Rt. Hon. Isa Mohammed Ashiru Kudan (Sarkin Bai Zazzau), ya amince da naɗin wasu fitattun mutane da za su jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027.
A cikin sanarwar naɗin da ya sanya wa hannu, Ashiru ya bayyana cewa waɗanda aka naɗa sun haɗa da ƙwararrun malamai, ’yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasar da ke da ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati da kuma mobilization na al’umma.
Dr. John Markus Ayuba ne aka naɗa Darakta-Janar na kwamitin. Ayuba malami ne, ƙwararren ma’aikacin banki kuma tsohon ma’aikacin gwamnati. Yana da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanar da Kasuwanci daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda aka bayyana cewa ya yi fice a jarabawar tantance ɗaliban PhD.
Ya kuma yi wa ABU karatun shekara bakwai tsakanin 1981 zuwa 1988, kafin ya shiga harkar banki inda ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Sashen Bankin Kamfanoni, Kasuwanci da Dillalan Arewa (Corporate, Commercial and Retail Banking – North) a tsohuwar Diamond Bank.
Ayuba ya kuma taɓa zama Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kaduna a zamanin marigayi Gwamna Patrick Yakowa, sannan ya zama Kwamishinan Albarkatun Ruwa a gwamnatin Gwamna Mukhtar Ramalan Yero. A zaɓen 2023 kuma, ya kasance ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar PDP a Kaduna.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙwarewarsa a fannin ilimi, kuɗi da siyasa, tare da tushensa da kuma tasirinsa a yankin Zangon Kataf da Kudancin Kaduna, za su taimaka wajen ƙarfafa jagorancin yaƙin neman zaɓen.
A gefe guda kuma, Hon. Bashir Ibrahim Sakadadi ya samu muƙamin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da Ayyuka (Deputy Director General, Operations).
Sakadadi, wanda aka bayyana a matsayin gogaggen jagoran siyasar matakin ƙasa, yana da alaƙa da al’ummar Sakadadi da ke yankin Sabon Gari na Jihar Kaduna. Ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan magoya baya, gudanar da harkokin tuntuba da kuma tsara ayyukan yaƙin neman zaɓe a matakin al’umma da ƙananan hukumomi.
Haka kuma, an naɗa Hon. Mukhtar Lawal Baloni a matsayin Sakataren Kwamitin.
Baloni tsohon ma’aikacin gudanarwar ƙaramar hukuma ne, wanda ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, daga bisani ya zama Shugaban ƙaramar hukumar, inda ya yi kusan shekaru shida a jere.
A lokacin da yake jagorantar ƙaramar hukumar, ya mayar da hankali kan bunƙasa kuɗaɗen shiga na cikin gida (Internally Generated Revenue – IGR), ilimi, kiwon lafiya, ayyukan jin ƙai da tallafawa al’umma, da kuma inganta ababen more rayuwa.
Sanarwar ta ce Baloni ya bar tarihin ayyukan ci gaba a ƙaramar hukumar tare da rashin barin bashin da zai gagari wanda ya gaje shi. Haka kuma, yana da faɗaɗɗun alaƙoƙin siyasa a cikin birnin Kaduna.
Ashiru ya ce waɗannan naɗe-naɗe sun haɗa ƙwarewar gudanar da mulki, ilimi da harkokin kuɗi, ƙwarewar tattara magoya baya a matakin ƙasa da kuma gogewar shugabancin ƙananan hukumomi, domin kafa ƙwararren kwamiti da zai jagoranci yaƙin neman zaɓensa.
Ya bayyana cewa tawagar za ta mayar da hankali kan gudanar da kamfen mai tsari, ƙwarewa da kuma mai la’akari da muradun jama’a.

No comments