Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki Uku Masu Sauya Fannin Wuta, Noma Da Muhalli

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sake nuna ƙudirinsa na sauya fasalin tattalin arziki da ci gaban jihar bayan sanya hannu kan wasu ...


Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sake nuna ƙudirinsa na sauya fasalin tattalin arziki da ci gaban jihar bayan sanya hannu kan wasu muhimman dokoki guda uku da ake sa ran za su kawo gagarumin sauyi a fannin wutar lantarki, noma da kuma kare muhalli.

Dokokin da gwamnan ya amince da su sun haɗa da Dokar Wutar Lantarki ta Jihar Kaduna ta 2026 da dokar asusun bunƙasa noma ta Kaduna (KADFund) ta 2025, da kuma dokar 
hukumar ba da Shawara Kan Sauyin Yanayi ta Jihar Kaduna ta 2026.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar, ya bayyana cewa sabbin dokokin za su samar da ingantaccen tsari da zai taimaka wajen jawo masu zuba jari, ƙarfafa samar da abinci, da kuma magance kalubalen sauyin yanayi.

Maiyaki ya ce dokar wutar lantarki za ta bai wa jihar damar tsara da kula da harkokin samarwa da rarraba wutar lantarki, tare da bude kofar zuba jari ga kamfanoni masu zaman kansu da bunkasa amfani da makamashi mai sabuntawa.

Haka kuma, ya ce dokar KADFund ta samar da wani asusu na musamman da zai tallafa wa manoma, kungiyoyin hadin gwiwa da masu harkokin kasuwancin noma ta hanyar ba su tallafi, rance mai sauki da kuma samar da muhimman ababen more rayuwa.

A bangaren muhalli kuwa, sabuwar dokar sauyin yanayi za ta taimaka wajen tsara manufofi da dabarun kare muhalli, nemo tallafin ayyukan sauyin yanayi da kuma tabbatar da cewa an hada batutuwan muhalli cikin shirye-shiryen ci gaban jihar.

Da yake karin haske kan muhimmancin dokokin, Mataimakin Babban Hafsan Ma’aikatan Gwamna mai kula da harkokin Shari’a da Majalisa, Dakta Mustapha Musa, ya bayyana cewa wannan na daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatin Uba Sani ta kawo domin samar da ci gaba mai dorewa da inganta rayuwar al’umma.

Ya ce dokokin za su taimaka wajen fadada samun wutar lantarki, bunkasa noma, karfafa tattalin arziki da kuma gina cibiyoyi masu dorewa da za su anfani al’ummar Kaduna na tsawon lokaci.

Gwamnatin jihar ta ce wadannan dokoki sun kara tabbatar da ƙudirin Gwamna Uba Sani na gina Kaduna mai ci gaba, wadda za ta kasance abar koyi a fannin zuba jari, samar da abinci da kuma kare muhalli a Nijeriya.
 

No comments