Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Kan Ebola, Ya Amince da Naira Biliyan 10 Don Shirin Bada Kariya

Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa Kwamitin Musamman na Fadar Shugaban Ƙasa kan Shirin Kariya daga Cutar Ebola da Sauran Barazana...


Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa Kwamitin Musamman na Fadar Shugaban Ƙasa kan Shirin Kariya daga Cutar Ebola da Sauran Barazanar Lafiyar Jama’a, tare da bayar da umarnin sakin naira biliyan 10 domin shirye-shiryen gaggawa.

A cewar sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, kuɗaɗen za su taimaka wajen ƙarfafa shirye-shiryen Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) da kuma ayyukan da suka shafi tunkarar duk wata barazanar gaggawa ga lafiyar al’umma.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne zai jagoranci sabon kwamitin, wanda zai haɗa da wakilai daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban, da kuma wakilan jihohi.

Matakin ya biyo bayan sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da kuma Uganda.

Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya jagoranta domin nazarin irin shirin da Najeriya ta yi da kuma dabarun da za su hana cutar shiga ƙasar.

Daga cikin mahalarta taron akwai wakilai daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN), Hukumar Shige da Fice (NIS), Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA), da gwamnatin jihar Legas.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci dukkan jihohin da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa da kuma manyan hanyoyin shiga ƙasar daga ƙasashen waje da su gabatar da tsare-tsarensu, buƙatun kuɗi da irin tallafin da suke buƙata domin aiwatar da matakan kariya cikin haɗin gwiwa.

A cikin matakan da aka sanar za a ɗauka akwai ƙara tsaurara binciken fasinjoji a dukkan filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, ciki har da duba zafin jiki da tsara yadda jama’a ke shiga da fita.

Haka kuma za a ƙarfafa sa ido kan fasinjojin da ke shigowa ta wasu hanyoyin jiragen sama da gwamnati ta ayyana a matsayin masu haɗari, ciki har da Air Uganda, RwandAir, Air Tanzania, Air Angola, Kenya Airways da Ethiopian Airlines.

Gwamnatin ta ce za a gaggauta bude cibiyoyin killace marasa lafiya da wuraren tura waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a filayen jiragen saman Legas da Abuja, kafin daga baya a faɗaɗa tsarin zuwa sauran filayen jiragen saman ƙasar.

Sauran matakan sun haɗa da wajabta cike bayanan lafiyar matafiya ta hanyar tsarin QR Code kafin su iso ƙasar idan sun fito ko suka bi ta ƙasashen da aka ayyana masu haɗari, da kuma tsaftace dakunan tashi da saukar jirage, wuraren kaya da sauran sassan filayen jiragen sama.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci kwamitin da ya tattauna da hukumomin tsaro, diflomasiyya da sufurin jiragen sama kan yiwuwar ɗaukar ƙarin matakan da suka shafi zirga-zirgar jirage daga ƙasashen da cutar ta bulla ko waɗanda aka sanya cikin jerin masu haɗari.

Bugu da ƙari, kwamitin zai duba yiwuwar ware wasu filayen jiragen sama ko tashoshi na musamman domin karɓar jiragen da ake ganin suna da haɗari, tare da nazarin sauya lokutan saukar wasu jirage domin rage haɗuwar fasinjojin da ake sa ran za su buƙaci ƙarin bincike da sauran matafiya.
 

No comments