● An Cafke Kwamandojin Boko Haram 7 Da Suka Dawo Daga Hajji Ta Hanyar Bayanai Na NIMC — Minista Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar Dokar Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta shekarar 2026, a wani mataki da gwamnati ta bayyana a matsayin babban sauyi wajen inganta tsarin tantance ‘yan kasa, tsaro da bunkasa tattalin arzikin zamani na Najeriya.
An gudanar da bikin sanya hannun ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a gaban Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, da Darakta Janar na NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote.
Da yake jawabi, Ministan Harkokin Cikin Gida ya ce sabuwar dokar za ta taimaka matuka wajen karfafa tsarin tsaro, inda ya bayyana cewa an samu nasarar cafke wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram da ISWAP guda bakwai a filin jirgin saman Katsina yayin da suke dawowa daga aikin Hajji a makon da ya gabata, sakamakon hada bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice da kuma tsarin yan sanda na kasa da kasa (Interpol).
Tunji-Ojo ya ce a baya bayanan gwamnati sun kasance a rarrabe, amma yanzu ba zai yiwu mutum ya samu fasfo na Najeriya ba tare da an tantance bayanansa daga NIMC ba. Ya kara da cewa sabuwar dokar za ta inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomi tare da dakile satar bayanai, ta’addanci da sauran miyagun laifukan.
Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yabawa Shugaba Tinubu kan amincewa da dokar, yana mai cewa ta dace da bukatun tsaro da ci gaban kasa a wannan zamani. A nata bangaren, Darakta Janar ta NIMC ta bayyana sabuwar dokar a matsayin wani gagarumin ci gaba da zai bai wa Najeriya damar gina ingantaccen tsarin shaidar dan kasa na zamani da zai saukaka samar da ayyukan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

No comments