Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NAZARI: Yadda Sabbin Matakan Da CBN Ya Ɗauka Za Su Daƙile Damfara A Hanyoyin Hahahadar Biyan Kuɗi Ta Intanet

Daga Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) na ƙara ƙarfafa yaƙi da masu damfara ta intanet, ta hanyar bijiro da sabbin ƙa’idoji...

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) na ƙara ƙarfafa yaƙi da masu damfara ta intanet, ta hanyar bijiro da sabbin ƙa’idojin da ya fitar kan ayyukan biyan kuɗi nan take, wanda aka fi sani da 'instant payment'.
 
Waɗannan ƙa’idoji dai an bayyana su a cikin takardar manufofin bankin, waɗanda suka ƙunshi matakai masu yawa da nufin ƙarfafa tsarin biyan kuɗi nan take, inganta tsaron mu’amaloli, kare haƙƙin masu amfani,   yadda za a tsaftace tsarin ya yi daidai da tsari da ƙa’idojin duniya.

Waɗannan sabbin dokoki kan ayyukan biyan kuɗi nan take na da fatan za su rage damfara ta hanyoyin biyan kuɗi na zamani, tare da bai wa kwastomomi damar samun ƙarin iko kan asusun su.

Sabbin dokokin sun bai wa kwastomomi damar zaɓar su kashe damar tura kuɗi nan take daga asusun su na wani lokaci, ko da yake har yanzu za su iya yin irin wannan ciniki ta hanyar zuwa banki da kan su.

A cikin wata sanarwa ta baya-bayan nan, CBN ya bayyana cewa tsarin shiga ko ficewa daga amfani da wannan sabis dole ne ya kasance yana da kariya ta hanyar ingantacciyar tantancewa mai matakai da dama, wadda a Turance ake kira 'multi-factor authentication'.

Sannan kuma, duk sabbin asusu da aka buɗe za a saka su kai-tsaye cikin tsarin biyan kuɗi nan take, amma kwastomomi na da damar sauya wannan zaɓi daga baya.

A ɓangaren bankuna kuma, ana buƙatar su bi wannan umarni ba tare da gazawa ba, tare da bai wa kwastomomi damar saita ƙarancin iyakar adadin kuɗin da za su iya turawa, bisa ga tantancewa da kimanta haɗarin da ka iya afkuwa yayin hahahada, yayin da iyakokin da doka ta tanada za su ci gaba da aiki. 

Sai kuma tabbatar da cewa cibiyoyin kuɗi za su samar da tsarin sa-ido kan damfara a ainihin lokaci, tare da ƙarfafa hanyoyin tantance sahihancin mutum wajen buɗe asusun yanar gizo ko sake kunna asusun da aka dakatar masa.

CBN ya kuma umarci cewa Manhajojin Bankin Hannu su kasance ana haɗa su da na’ura guda ɗaya kacal a lokaci guda. Idan aka kunna manhajar a sabuwar na’ura, za a sanya mata iyakar ciniki na wucin gadi na Naira 20,000 na tsawon awanni 24 na farko.

A ƙarƙashin tsohon tsarin, ba a tilasta wa cibiyoyin kuɗi su samar da wata hanya a cikin manhajojin bankin su da za ta bai wa kwastomomi damar shiga ko fita daga tsarin biyan kuɗi nan take da kan su ba.

Amma sabbin ƙa’idojin sun buƙaci cibiyoyin kuɗi su bai wa kwastomomi damar ficewa daga tsarin a kowane lokaci, bayan an kammala tantancewa mai matakai da dama.

Sannan bisa tanade-tanaden sabbin ƙa’idojin, za a shigar da kwastomomi cikin tsarin biyan kuɗi nan take, wato otimatik.
 
Sai dai kuma wanda ya fice daga tsarin ba zai iya tura kuɗi ta intanet kai tsaye daga asusun sa ba, amma dai zai iya yin hakan ta hanyar zuwa reshen banki da kan sa.

Kafin kafa waɗannan ƙa’idoji, iyakar adadin kuɗin da mutum zai iya turawa su ne ce Naira miliyan 25 ga mutum ɗaya, yayin da kamfanoni ke da iyakar Naira miliyan 250, ba tare da damar kwastoma ya saita tasa iyakar ba.

Su dai waɗannan sabbin ƙa’idojin, za su bai wa mutane da kamfanoni damar rage ko ƙara iyakar adadin cinikin su gwargwadon buƙata, bayan an gudanar da ƙarin bincike da bin matakan kula da haɗari daga cibiyar kuɗin.

Domin tabbatar da tsaro, sabuwar iyakar ciniki ba za ta fara aiki ba sai kwastoma ya kammala tantancewa mai matakai da dama.

Masana harkokin kuɗi sun bayyana cewa ƙa’idojin sun kuma yi tanadi ga yanayin da mutum zai buɗe sabon asusu ta intanet ko kuma ya sake kunna tsohon asusun intanet. A irin wannan yanayi, za a yi amfani da ƙarin matakan tsaro kamar gwajin tabbatar da kasancewar mutum a zahiri, tabbatar da bayanan BVN/NIN kai tsaye, da kuma amfani da hanyoyin tantancewa na zamani kamar na’urar tantance yatsa ko fuska, gamsasshen bayani a rubuce a shafin intanet ko a zahiri a takarda.

Sun kuma bayyana tantancewar ido-da-ido a matsayin hanyar tsaro ta amfani da bayanan gwajin salsalar halitta, wadda ke tabbatar da cewa kai ɗin, kai ne a da gaske, kuma a zahiri, ba hoto ba, bidiyo ba, ko hoton ƙarya da fasahar zamani ta samar ba.
 
Wannan tsarin yana duba abubuwa kamar yanayin fata, motsin ido da zurfin fuska domin hana masu damfara amfani da bayanan bogi.

Sabbin ƙa’idojin sun kuma ƙunshi tsarin sa-ido kan damfara wanda ke tilasta wa cibiyoyin kuɗi samar da cikakken tsarin gano damfara da aiki a kai wanda zai shafi dukkan hanyoyin shiga da fitar kuɗi.

Wannan zai taimaka wajen daƙile mu’amaloli masu kama da haɗari da barazana nan take, tare da bayar da damar gano damfara da ɗaukar mataki cikin gaggawa.

A tsohon tsari, kwastomomi na iya amfani da manhajar bankin su a na’urori daban-daban a lokaci guda. Amma sabbin ƙa’idojin sun hana hakan, inda aka ƙayyade cewa manhajar banki za ta kasance a na’ura guda ɗaya kacal.
Idan aka sauya zuwa sabuwar na’ura, tsohuwar na’urar za a cire ta daga tsarin, sannan a sake kunna sabuwar bayan an kammala tantancewa.

CBN ya kuma gabatar da waɗannan matakai ga manhajojin hadahadar kuɗi ta hannu da tsarin intanet.

Ƙa'idojin Sabbin Masu Asusu:

Bayan kunna manhajar banki ta hannu, za a taƙaita shigar kuɗi da fitar kuɗi a cikin awanni 24 na farko, kuma iyakar ciniki ba zai wuce Naira 20,000 ba.

Masu Tsoffin Asusu: 

Bayan kunna manhajar banki a wata na’ura, za a taƙaita fitar kuɗi na awanni 24 na farko, kuma iyakar ciniki ba zai wuce Naira 20,000 ba.

Haka kuma, shiga bankin intanet a karon farko daga sabuwar na’ura zai buƙaci ƙarin matakan tantancewa masu ƙarfi.

Yana da muhimmanci a jaddada muhimmancin waɗannan ƙa’idoji wajen yaƙi da damfarar intanet da sauran matsalolin da ke rage amincewar jama’a ga tsarin kuɗi.

Haka kuma ya dace a yaba wa CBN, saboda hangen nesa da ya nuna wajen samar da sabbin ƙa’idojin ayyukan biyan kuɗi nan take ga cibiyoyin kuɗi, domin wannan wani babban mataki ne na kare mu’amalolin kuɗi na zamani a faɗin ƙasar.

Daga ranar 1 ga Yuli, 2026, cibiyoyin kuɗi za su fara aiwatar da waɗannan matakai. Daga cikin abubuwan da ƙa’idojin suka tanada akwai gudanar da cikakken binciken tsaro da tantancewa, 'Data Protection Impact Assessments' (DPIAs) domin tabbatar da bin dokar kare bayanai ta Nijeriya ta shekarar 2023, musamman saboda buƙatar amfani da hanyoyi kamar tantancewa mai matakai da dama, tantance fuska, da kuma ci gaba da bibiyar mu’amaloli da hadahadar kuɗi. 

No comments