Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sake Gina Gadar STORE Na Giwa Ya Tabbatar Da Kyawawan Manofofin Gwamna Uba Sani

Da yake jagorantar tawagar ‘yan jaridar wajen duba ayyukan gwamnatin jihar Kaduna, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki, ...


Da yake jagorantar tawagar ‘yan jaridar wajen duba ayyukan gwamnatin jihar Kaduna, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce manufar ziyarar ita ce bai wa kafafen yaɗa labarai damar gani da idon su irin tasirin ayyukan da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Maiyaki ya bayyana cewa sake gina Gadar Store wani muhimmin mataki ne na gwamnatin Gwamna Uba Sani wajen bunƙasa yankunan karkara da inganta rayuwar al’umma.

“Wannan gada ba kawai hanyar ketarewa ba ce. Ta dawo da harkokin tattalin arziki, ta inganta samun kulawar lafiya, kuma ta sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki bayan sama da shekaru 20 na wahala,” in ji Maiyaki.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da za su ƙarfafa tattalin arziki, inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar Kaduna.

Mazauna yankin sun bayyana cewa sake gina Gadar Store ba kawai aikin titi ba ne, illa wata babbar nasara ce da ta dawo da fata, walwala da ci gaban tattalin arziki ga dubban al’ummar yankin Giwa da maƙwabtansu.

Suka ce gina Gadar Store da ke kan hanyar Marabar Yakawada zuwa Kaya, inda suka ce aikin da gwamnatin Gwamna Uba Sani ta aiwatar ya kawo ƙarshen wahalhalun da suka shafe fiye da shekaru 20 suna fama da su.

Mazaunan sun bayyana hakan ne yayin da tawagar ‘yan jarida ta kai ziyarar gani da ido kan ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa. Sun ce gadar ta zama wata muhimmiyar hanyar haɗin kai da ta dawo da zirga-zirga, kasuwanci da harkokin noma a yankunan da a baya kan kasance cikin ƙunci musamman a lokacin damina.

A zantawarsa da manema labarai Wani direba mai kabu-kabu daga ƙauyen Kaya, Malam Shehu Muharazu, ya ce rugujewar gadar a baya na haddasa matsaloli masu yawa ga matafiya da masu safarar kaya.

A cewarsa, duk lokacin da damina ta yi ƙarfi, hanyar kan zama ba za a iya bi ba, lamarin da ke hana zirga-zirga tare da durƙusar da harkokin kasuwanci a yankin.

“Mun sha wahala sosai tsawon shekaru. A wasu lokutan sai mun bi ta Sabuwa da Funtua a Jihar Katsina kafin mu isa inda za mu je. Hakan yana ƙara mana kuɗin man fetur da kuma haɗurran hanya. Yanzu komai ya sauya,” in ji shi.

Shi ma wani manomi daga Marabar Yakawada, Malam Ibrahim Muhammadu, ya bayyana cewa matsalar gadar ta dade tana hana manoma gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.

Ya ce a lokuta da dama manoma kan makale a bakin gadar bayan dawowa daga gonaki saboda yawaitar ruwa, abin da ke janyo jinkiri da asarar lokaci.

A nasa ɓangaren, Malam Muhammad Aminu daga garin Gadagau ya ce sake gina gadar ta kawo sauyi mai yawa a fannin kiwon lafiya, musamman wajen kai marasa lafiya cikin gaggawa zuwa manyan asibitoci.

Ya ce a baya, matsalar hanyar kan janyo jinkirin kai mata masu juna biyu da sauran marasa lafiya zuwa cibiyoyin lafiya, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da za a iya kaucewa.

“Yanzu an samu sauƙi sosai wajen kai marasa lafiya asibiti cikin lokaci. Wannan gada ta ceci rayuka da dama,” in ji shi.
 

No comments