Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ya Gargaɗi ’Yan Nijeriya Kan Cin Zarafin Takardun Naira

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake yin gargaɗi ga al’umma kan muhimmancin mutuntawa da kuma kula da takardun kuɗin ƙasar, yana mai jaddada...


Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake yin gargaɗi ga al’umma kan muhimmancin mutuntawa da kuma kula da takardun kuɗin ƙasar, yana mai jaddada cewa duk wani nau’i na cin zarafin Naira ya saɓa wa doka.

A cikin wani saƙon wayar da kai da ya fito daga Ofishin Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya lissafa wasu daga cikin abubuwan da ya haramta wa jama’a aikatawa da takardun Naira.

Abubuwan Da Aka Hana Yi Da Takardun Naira Su Haɗa Da;

• Kekketa Naira

• Dunƙune Naira

• Buga kuɗaɗen jabu

• Shafa wa Naira datti

• Liƙa Naira a wuraren bukukuwa

CBN ya tunatar da jama'a cewa Naira wata muhimmiyar alama ce ta ƙasa da ke wakiltar martaba da tattalin arzikin Nijeriya, don haka ya zama wajibi a kiyaye ta da kuma amfani da ita yadda doka ta tanada.

Bankin ya bayyana cewa cin zarafin takardun kuɗi na haifar da lalacewarsu cikin sauri, lamarin da ke ƙara wa gwamnati nauyin kashe kuɗaɗe wajen sake buga sababbin takardun kuɗi.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su daina halayen da ke rage darajar kuɗin ƙasa, musamman a wuraren bukukuwa da tarurruka inda ake yawan amfani da takardun kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

CBN ya ƙara da cewa mutunta Naira wani bangare ne na kishin ƙasa da kuma gudummawar da kowane ɗan Nijeriya zai iya bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

“A tuna, darajar Naira darajar ƙasar mu ce.”

Saƙon ya jaddada aniyar bankin na ci gaba da wayar da kan jama’a kan yadda ya kamata a riƙa amfani da kuɗin ƙasa.
 

No comments