Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cardoso Ya Ƙaddamar Da Ƙungiyar Jakadun Naira Na CBN

• Ya gargaɗi ’yan Nijeriya su daina wulaƙanta takardun naira Daga Ashafa Murnai Barkiya Gwamnan Babban Bankin Njeriya (CBN), Olayemi Cardoso...


• Ya gargaɗi ’yan Nijeriya su daina wulaƙanta takardun naira

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Gwamnan Babban Bankin Njeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN, wani shiri da aka samar domin wayar da kan al’umma, musamman matasa kan muhimmancin kare daraja da martabar takardun Naira da kuma kula da yadda ake amfani da ita.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ƙungiyar da ta ƙunshi ɗaliban makarantun sakandare a Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) Cardoso ya ce,
“Darajar Naira ta fi ƙarfin darajar takardar da aka yi ta da shi. Ita ce kuɗin da doka ta amince da su a Nijeriya. Naira na sauƙaƙa harkokin kasuwanci, tallafa wa ayyukan tattalin arziki, ba da damar ajiya da zuba jari, sannan tana nuna asalin ƙasa da ikonmu a matsayinf al’umma.”

Ya ƙara da cewa kowace takardar kuɗi tana ɗauke da tarihin ƙasa, domin tana ƙunshe da hotunan fitattun ’yan Nijeriya, alamomin ƙasa da kuma abubuwan kariya da aka tsara domin tabbatar da amincewar jama’a ga tsarin kuɗin ƙasar nan.

Cardoso ya ci gaba da cewa, “kowane ɗan Nijeriya yana da alhakin girmama Naira.”

Gwamnan na CBN ya bayyana cewa CBN na ci gaba da kashe kuɗaɗe masu yawa wajen samar da tsabtatattun takardun kuɗi masu ƙarfi da kariya domin biyan buƙatun tattalin arzikin ƙasa.

Daga nan sai ya yi gargaɗin cewa lalata takardun kuɗi, yin rubutu a kan su ko rashin kula da su na sa su lalace da wuri, lamarin da ke ƙara tsadar biyan kuɗin sauya su tare da kawo cikas ga ingancin zagayawar kuɗi a ƙasa.

Ya jaddada cewa kare kuɗin ƙasa ba aikin CBN kaɗai ba ne, illa dai “wani nauyi ne na ƙasa da ya rataya a wuyan kowane ɗan Nijeriya.”

Mataimakiyar Gwamnan CBN mai kula da Ayyuka, Emem Usoro, ta bayyana shirin a matsayin wani mataki da ke nuna ci gaba da ƙoƙarin da CBN ɗin ke yi wajen kare ɗaya daga cikin manyan kadarorin ƙasa, wato Naira.

Ta ce, “Duk ƙasa tana alfahari da kuɗin ta, domin ba wai hanyar musayar kaya kawai ba ce, naira na wakiltar ikon ƙasa, kwanciyar hankali na tattalin arziki, amincewar jama’a da kuma haɗin kan al’umma.”

Da take magana kan yadda ake cin zarafin kuɗi, ta ce rubutu a kan takardun Naira, ɗaure su da ƙarfe, watsa su yayin bukukuwa, duƙunƙune su a cikin aljihu da sauran hanyoyin lalata kuɗi suna rage tsawon lokacin da ake mu'amala da su tsakanin jama'a, tare da ƙara tsadar sauya adadin takardun nairar da suka lalace.

Ta bayyana cewa samun sauyi mai ɗorewa zai zo ne ta hanyar ilimantarwa, wayar da kai da kuma gina kyawawan ɗabi’u tun daga ƙuruciya.

Daraktan Ayyukan Kuɗi da Gudanar da Rassa na CBN, Adetona Adedeji, ya ce kare Naira “haƙƙin kowane ɗan Nijeriya ne,” yana mai cewa za a faɗaɗa wannan yaƙin neman wayar da kai zuwa sassa daban-daban na ƙasar domin daƙile munanan ɗabi'un watsa kuɗi a wurin bukukuwa da sauran hanyoyin cin zarafin naira.
 

No comments