Tsohon mai ba Shugaban Ƙasa shawara kuma Jakaden Nijeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Meziko, Reno Omokri, ya kare ayyukan gwamnatin Shugaba Bola...
Tsohon mai ba Shugaban Ƙasa shawara kuma Jakaden Nijeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Meziko, Reno Omokri, ya kare ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya fi ƙarfi a yanzu idan aka kwatanta shi da lokacin da Shugaban ya hau mulki a shekarar 2023.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafukan sa na soshiyal midiya, Omokri ya kawo wasu alƙaluman tattalin arziki da shirye-shiryen gwamnati waɗanda ya ce sun nuna cigaba a tattalin arzikin ƙasar nan da kuma walwalar al'ummar Nijeriya.
A cewar sa, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, wadda take kashi 23 cikin ɗari kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki, ta ragu zuwa kashi 15.9 cikin ɗari a halin yanzu. Haka kuma, ya ce mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan ya tashi daga N30,000 zuwa N70,000 a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Omokri ya ƙara da cewa kuɗaɗen da ake raba wa jihohi da ƙananan hukumomi duk wata ta hannun Kwamitin Rabon Kuɗi ga Asusu na Tarayya (FAAC) sun ƙaru sosai.
Ya ce, "Kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki, FAAC na raba kimanin naira biliyan 700 a duk wata ga jihohi da ƙananan hukumomi. A yau kuwa, adadin ya kai kusan naira tiriliyan 2.1 a wata."
Ya bayyana cewa wannan ƙarin kuɗin da ake rabawa ya inganta ƙarfin tattalin arzikin gwamnatocin jihohi, yana mai cewa yayin da jihohi da dama suka sha fama da biyan albashi a shekarar 2022, a yanzu dukkan jihohin ƙasar nan suna iya biyan albashin ma'aikatan su.
Jakaden da aka naɗa ya kuma yi magana kan ajiyar kuɗaɗen ƙasar nan a ƙasashen waje, inda ya ce sun kai dala biliyan 51.04, wanda ya bayyana a matsayin mafi girman adadin da aka samu cikin shekaru 17 da suka gabata.
A ɓangaren ilimi kuwa, Omokri ya yaba da aikin Hukumar Bada Lamuni ga Ɗalibai (NELFUND), yana mai cewa kusan kashi ɗaya bisa uku na ɗaliban jami'o'in Nijeriya su miliyan 3.1 sun amfana da tsarin bashin karatu da gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar.
Ya kuma yi nuni da kwanciyar hankali da aka samu a jami'o'in ƙasar nan, inda ya ce cikin shekaru uku da suka gabata ba a samu yajin aiki na ƙasa baki ɗaya daga Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ba.
Ya ce, "A wannan gwamnati, kwas na shekaru huɗu yana ci gaba da kasancewa kwas na shekaru huɗu."
Omokri ya kuma yaba da ayyukan gine-ginen manyan hanyoyi da gwamnatin ke yi, yana mai ambaton ayyukan tituna kamar Babban Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, Babban Titin Illela zuwa Sakkwato zuwa Badagiri da Hanyar da ta yankin Sahara a matsayin hujjojin ƙoƙarin gwamnati na inganta hanyoyin sufuri da haɗa sassa daban-daban na ƙasar nan.
Har ila yau, ya yi nuni da cewa Nijeriya ta sauya daga kasancewa ƙasa mafi yawan shigo da man fetur da aka tace a Afrika a shekarar 2022 zuwa zama mafi yawan mai fitar da irin wannan man a yankin Yammacin Afrika.
A cewar sa, tattalin arzikin ƙasar ya samu cigaban GDP da kuma rarar ciniki a jere har tsawon kwata 12, abin da ya taimaka wajen ƙara ƙarfin masana'antun cikin gida.
Omokri ya buƙaci 'yan Nijeriya da su yi la'akari da cigaban ƙasar bisa ga alƙaluman tattalin arziki da abubuwan da ake gani a fili.
Ya ce, "Ina kira ga 'yan Nijeriya da su sanya al'amurra a ma'aunin su na gaskiya, kuma kada su bari masu yaɗa bayanan da ba su da tushe su ruɗe su. Babu shakka, Nijeriya ta fi yadda take a yau idan aka kwatanta ta da shekarar 2023."
Wannan furuci nasa yana zuwa ne a yayin da ake ci gaba da muhawara a tsakanin al'umma kan tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, musamman dangane da tsadar rayuwa da kuma walwalar 'yan Nijeriya baki ɗaya.

No comments