Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ƙaddamar da babban aikin samar da ruwan sha da ya haɗa garuruwan Karu, Orozo, Jikwoyi, ...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ƙaddamar da babban aikin samar da ruwan sha da ya haɗa garuruwan Karu, Orozo, Jikwoyi, Kurudu da sauran yankunan da ke kewaye da su a birnin tarayya Abuja.Sanata Shettima ya bayyana cewa wannan aiki wata babbar alama ce ta fata ga mazauna yankunan karkara da na bayan gari a Abuja, yana mai cewa aikin ya cika alkawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na kawo ƙarshen watsi da waɗannan yankuna ƙarƙashin manufofin Renewed Hope Agenda.
Ya ƙara da cewa ajandar Renewed Hope wata muhimmiyar yarjejeniya ce tsakanin gwamnatin Tinubu da al’ummar Nijeriya domin inganta rayuwar jama’a ta hanyar samar da muhimman abubuwan more rayuwa.
A jawabinsa yayin ƙaddamar da aikin, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana farin cikin Shugaba Tinubu tare da godiya ga Allah bisa kammala wannan babban aikin samar da ruwan sha, wanda ya ce ya cika alkawarin da aka yi wa al’ummar yankunan da abin ya shafa.




No comments