Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya halarci bikin cika shekaru 70 da kuma bikin bankwana da aiki na Sarkin Lafia, Mai Marta...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya halarci bikin cika shekaru 70 da kuma bikin bankwana da aiki na Sarkin Lafia, Mai Martaba Justice Sidi Bage Muhammad (mai ritaya), wanda aka gudanar a birnin Lafia na Jihar Nasarawa.
A jawabinsa, Sanata Shettima ya bayyana cewa samun zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaban Najeriya na dogara ne da shugabannin da ke fifita adalci, haɗin kai da jin daɗin jama'a fiye da son zuciya da neman iko.
Ya yabawa Sarkin Lafia na 16, inda ya bayyana shi a matsayin abin koyi na shugabanci nagari da Najeriya ke buƙata a dukkan yankunanta.
A yayin ziyararsa ta Lafia, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma kaddamar da titin Maimatasa-Gemeri-Federal University Road da ke Lafia, tare da wani sabon titin kilomita biyar mai suna Kashim Shettima Road, domin inganta harkokin sufuri da ci gaban al'umma a babban birnin jihar.






No comments