Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abdul'aziz Ya Karbi Baƙuncin Sakataren Gwamnatin Yobe A Abuja

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai” Abdul’aziz Abdul’aziz, ya bayyana jin daɗin sa da k...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai” Abdul’aziz Abdul’aziz, ya bayyana jin daɗin sa da karɓar baƙuncin Muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Mohammed Goje, wanda ya kai masa ziyara tare da abokin sa kuma abokin siyasa, Farfesa Sheriff Almuhajir, Darakta Janar na Bankin Microfinance na Jihar Yobe.

Ganawar ta kasance mai armashi, inda Aka tattauna batutuwa masu zurfi da suka shafi aiki da shugabanci.

Abdul'aziz ya bayyana cewa hangen nesan Dakta Goje da kuma kishin sa ga aiki sun daga cikin dalilan da suka sa Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni ya ba shi wannan muhimmin matsayi.

Ya kuma gode wa Gwamna Buni bisa wannan zaɓi mai kyau, tare da yi wa Dakta Goje fatan alheri a sabon aikin da aka ɗora masa.

 

No comments