Haɗin gwiwar jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin Gwamnatin Tarayya ya yi nasarar kama makamai da alburusai da ake zargin an shirya kai wa ’ya...
Haɗin gwiwar jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin Gwamnatin Tarayya ya yi nasarar kama makamai da alburusai da ake zargin an shirya kai wa ’yan ta’adda a Jihar Kogi.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na jihar, rundunar Hybrid Forces ta ONSA, DSS da kuma Rundunar Sojin Najeriya ta 12 Brigade.
Rahotannin sirri sun nuna cewa an gano wani shiri na safarar makamai zuwa hannun miyagun laifuffuka. Bayan sa ido da aka yi na sama da makonni biyu, jami’an tsaro sun cafke mutum uku a Jihar Sokoto tare da gano hanyar safarar makaman.
Daga cikin makaman da aka kama akwai bindigogi kirar AK-47 guda biyu, magazin na AK-47, harsasai 67 na 7.62mm, bindigogi ƙanana guda biyu, harsasai 12 na bindigogin hannu da kuma kayan sojoji. An kuma ƙwace motar Golf 2 da ake amfani da ita wajen jigilar makaman.
Gwamnatin jihar ta ce makaman na daga cikin yunƙurin da ragowar ’yan ta’adda ke yi na sake ƙarfafa kansu bayan mummunan farmakin da jami’an tsaro suka yi musu, ciki har da kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga Kachalla Bastuji.
Ta yabawa Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa Kogi ba za ta zama mafakar ’yan ta’adda ba, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka.

No comments