Sakamakon ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Uba Sani ta yi, wanda ya farfado da harkar noma da kasuwanci a yankin, Mazauna Ƙaramar Hukumar Giwa...
Sakamakon ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Uba Sani ta yi, wanda ya farfado da harkar noma da kasuwanci a yankin, Mazauna Ƙaramar Hukumar Giwa da ke jihar Kaduna sun bayyana jin daɗin su, tare da yaba wa Gwamna Uba Sani bisa manyan ayyukan raya ƙasa da gwamnatin sa ke aiwatarwa, waɗanda suka ce sun fara sauya fasalin yankin.Mazauna yankin sun bayyana cewa bayan shekaru masu yawa na fama da ƙarancin ababen more rayuwa da rashin manyan ayyukan gwamnati, yanzu suna ganin sauyi a zahiri sakamakon ayyukan da gwamnatin Uba Sani ke gudanarwa.
Daga cikin ayyukan da suka fi ɗaukar hankalin jama'a akwai gina babbar kasuwar hatsi ta Giwa da aikin titunan cikin garin Giwa, da kuma sake gina gadar da ta haɗa garin Giwa da Yakawada.
Yayin wata ziyarar duba ayyukan da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na Jihar Kaduna tare da Kwamishinan Lafiya suka kai yankin, mazauna garuruwan sun bayyana cewa ayyukan sun nuna kudirin Gwamna Uba Sani na tabbatar da ci gaba ya kai ga kowane lungu da sako na jihar.
Manoma da 'yan kasuwa sun kuma bayyana cewa ingantattun hanyoyi da ababen more rayuwa za su rage musu kashe kudaden sufuri da bata lokaci, lamarin da zai kara bunkasa tattalin arzikin yankin.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa karamar hukumar Giwa ba ta samu irin wadannan manyan ayyuka na gwamnati ba tsawon shekaru da dama, don haka suna matukar farin ciki da yadda gwamnatin yanzu ke mayar da hankali kan ayyukan da ke shafar rayuwar talakawa kai tsaye.
Sun kara yaba wa Gwamna Uba Sani bisa ƙoƙarinsa na kai ayyukan ci gaba zuwa karkara, tare da bayyana fatan cewa ayyukan da ake yi za su ƙara habaka tattalin arziki, samar da guraben ayyukan yi, da inganta rayuwar al'ummar Ƙaramar Hukumar Giwa baki ɗaya.
A zantawar sa da manema labarai Shugaban Karamar hukumar Giwa Dakta Ahmed Sama'ila Yakawada, yace Idan aka Kammala gina Kasuwa hatsi wanda Gwamna Uba Sani Ya bayar da Umarnin fara gina ta zata Zama irinta ta farko a yammacin Afarka wajen hada-hadar hatsi yana mai cewa Karamar hukumar Giwa ita kan gaba a jihar Kaduna wajen noman masara.
Akan hakan Ya yace babu abinda zasu cewa Gwamna Uba Sani Sai fatan Alkhari. A cewar sa Idan zabe ya yazo al'ummar yankin za su Fito ƙwansu da ƙwarƙwatar su wajen kaɗa masa ƙuru'u domin sake zama Gwamna a Karo na Biyu.
No comments