A yau a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya halarci taron addu’ar shekara-shekara da aka gudan...
A yau a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya halarci taron addu’ar shekara-shekara da aka gudanar tunawa da marigayiya Alhaja Abibatu Mogaji, mahaifiyar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A jawabinsa, Sanata Shettima ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tarbiyya da tasiri, wacce ta bar gagarumin tarihi da zai ci gaba da zama jagora ga al’umma da kuma zuriyarta. Ya ce rayuwarta ta kasance ta hidima, gina mutane da ƙarfafa cibiyoyi ba tare da hayaniya ba.
Haka kuma ya jaddada cewa irin tarbiyyar da ta ba ɗanta ne ya taimaka wajen fahimtar nauyin shugabanci da ya ke yi a yanzu, inda ya ke kallon mulki a matsayin amana ga talakawa da marasa murya.








No comments