Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ZAƁEN CIKE GURBI: Ɗan Takarar APC Ya Nuna Gamsuwa Da Tsarin Da Aka Yi

Daga Zubairu M Lawal, Lafia  Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbin Sanatan Nasarawa ta Arewa, Alhaji Halilu Emvulanza Aliyu, ya bayy...

Daga Zubairu M Lawal, Lafia 

Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbin Sanatan Nasarawa ta Arewa, Alhaji Halilu Emvulanza Aliyu, ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaɓen ke gudana, inda ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan shirye-shiryen da ta yi.

Da yake zantawa da manema labarai a ɗaya daga cikin rumfunan zaɓe, Emvulanza ya ce fitowar masu kaɗa ƙuri’a tana da armashi kuma abin ƙarfafa gwiwa ne, yana mai cewa jam’iyyar APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyya mai karɓuwa a faɗin jihar.

“Fitowar jama’a tana da kyau ƙwarai. Komai yana tafiya yadda ya kamata. APC sunan gida ne a Nasarawa, kuma hakan yana bayyana a yadda jama’a ke amsa kiran zaɓe,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa INEC kan yadda ta gudanar da shirye-shiryen zaɓen, yana mai cewa duk da ɗan jinkirin da aka samu wajen rabon kayan aiki, an kai su rumfunan zaɓe cikin lokaci kuma ba a samu manyan ƙorafe-ƙorafe ba.

“Zan ba INEC kashi 90 cikin 100 saboda yadda ta gudanar da aikin. Ya zuwa yanzu komai yana tafiya cikin tsari,” ya ƙara da cewa.
Game da hasashensa kan sakamakon zaɓen, Emvulanza ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai samu nasara.

“Da yardar Allah zan yi nasara a wannan zaɓe,” in ji shi.

Ɗan takarar ya ce abin da ya fi ba shi kwarin gwiwa shi ne irin ayyukan alheri da ya yi wa jama’a tsawon shekaru, yana mai cewa a dukkan gundumomi 35 na mazabar, mutane suna bayyana irin taimakon da ya taba yi musu.

Ya kuma tabbatar da cewa babu manyan matsalolin tsaro da suka taso yayin zaɓen, sai dai wani ɗan ƙaramin lamari da aka samu a yankin Wakama wanda jami’an tsaro suka shawo kansa.

A ƙarshe, Emvulanza ya yi kira ga al’ummar mazabar da su ci gaba da kasancewa masu zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan kammala zaɓen.

“Daga bayanan da muke samu daga Nasarawa Eggon, Wamba da Akwanga, komai yana tafiya cikin lumana. Ina kira ga jama’a su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya,” in ji shi.
 

No comments