Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sauya muƙaman mataimakan gwamnonin sa, inda aka fara aiwatar da sabbin muƙaman daga ranar 1 ga Yuni...
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sauya muƙaman mataimakan gwamnonin sa, inda aka fara aiwatar da sabbin muƙaman daga ranar 1 ga Yuni, 2026.
CBN ya bayyana sabbin naɗe-naɗen ne a shafin sa na yanar gizo, inda aka bayyana sabbin wuraren aiki ga Mataimakan Gwamnoni huɗu yayin da bankin ke ci gaba da kula da manufofin kuɗi, sa ido kan harkokin tsarin kuɗi da sauran muhimman ayyukan tattalin arzikin ƙasa.
A ƙarƙashin sabon tsarin, an sauya Dakta Muhammad Sani Abdullahi daga Daraktan Manufofin Tattalin Arziki (Economic Policy Directorate) zuwa jagorantar Sashen Ayyukan (Corporate Services).
Haka kuma sanarwar ta nuna cewa Philip Chukwuemeka Ikeazor ne zai karɓi ragamar Daraktan Manufofin Tattalin Arziki.
Sauyin ya kuma haɗa da canja Emem Nnana Usoro daga Sashen Ayyukan Kamfani zuwa kula da Ayyuka (Operations), yayin da Lamido Abubakar Yuguda ya tashi daga Sashen Ayyuka zuwa Daraktan Tabbatar da Daidaiton Tsarin Kuɗi (Financial System Stability Directorate).
Wannan sabon sauyin na zuwa ne yayin da Babban Bankin Najeriya ke ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa tsarin gudanarwar sa na cikin gida da inganta haɗin kai tsakanin sassan da ke da alhakin aiwatar da manufofi, sa-ido kan bankuna da kuma gudanar da harkokin cibiyar.
Ko da yake CBN bai bayyana takamaiman dalilan sauyin ba, irin waɗannan canje-canje na yawan faruwa a manyan cibiyoyi da hukumomin gwamnati domin amfani da ƙwarewar manyan jami’ai a fannoni daban-daban na aiki da kuma tallafa wa sabbin manufofi.
Daraktar Manufofin Tattalin Arziki na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da binciken tattalin arziki da tantance manufofi da ke taimakawa wajen yanke shawara kan ƙimar kuɗin ruwa, sarrafa hauhawar a farashi da sauran matakan manufofin kuɗi.
Sashen Ayyukan Kamfani kuwa yana kula da harkokin gudanarwa da ayyukan tallafi da ke tabbatar da tafiyar da ayyukan cibiyar cikin sauƙi da inganci.
Sashen Ayyuka ke da alhakin gudanar da ayyuka daban-daban da suka shafi aiwatar da ayyukan yau da kullum na bankin, ciki har da kula da kuɗaɗen ƙasa da kuma gudanar da tsarin biyan kuɗi.
Sai kuma Daraktan Tabbatar da Daidaiton Tsarin Kuɗi na sa-ido kan haɗurran da ka iya tasowa a fannin bankuna tare da tabbatar da lafiyar tsarin kuɗi baki ɗaya.
Wannan sauyin muƙamai na gudana ne a daidai lokacin da CBN ke aiwatar da gyare-gyare da nufin ƙarfafa amincewa da tsarin kuɗi, inganta tasirin dokoki da ƙa’idoji, da kuma tallafa wa daidaiton tattalin arzikin ƙasa.

No comments