Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kashe kuɗi kusan naira biliyan 250 a cikin shekarar 2026 domin gina sabbin ɗakunan kwanan ɗalibai a ma...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kashe kuɗi kusan naira biliyan 250 a cikin shekarar 2026 domin gina sabbin ɗakunan kwanan ɗalibai a manyan makarantun gaba da sakandare na ƙasar nan.
Wannan mataki na ƙunshe ne a cikin wani babban shiri na kyautata jin daɗin ɗalibai da kuma faɗaɗa damar samun ilimi mai inganci, wanda ake ganin shi ne jari mafi tsoka da aka taba zubawa a fannin gidajen ɗalibai a tarihin Nijeriya.
Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa wannan shiri zai magance matsalolin karancin masauki da ɗalibai ke fuskanta.
Za a kashe naira biliyan 100 wajen gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu ɗauke da gado 500 a kowace jami'a daga jami'o'i guda 50 a faɗin ƙasar nan. Kowanne aiki ɗaya an ƙiyasta shi a kan naira biliyan 2.
Za a gudanar da wasu ayyukan guda 24 na haɗin gwiwa da masu zuba jari masu zaman kansu, inda gwamnati za ta bayar da biliyan ɗaya, su kuma masu zuba jari su bayar da biliyan 3 a kowanne aiki. Wannan zai samar da masauki ga ɗalibai tsakanin 1,200 zuwa 1,500 a kowace makaranta.
Hukumar tallafa wa manyan makarantu ta TETFund ce za ta ɗauki nauyin samar da waɗannan kuɗaɗe, inda za a yi amfani da su wajen gina sabbi da kuma gyara tsofaffin ɗakunan kwanan ɗalibai da suka lalace.
Babban burin wannan shiri shi ne samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, tare da rage cinkoson ɗalibai a ɗaki ɗaya da ake samu a manyan makarantun ƙasar nan a halin yanzu.
"Wannan shiri ne da zai tabbatar da cewa ɗaliban mu sun samu wurin kwana mai tsafta da walwala, wanda hakan zai taimaka musu wajen mayar da hankali kan karatunsu." — Maruf Olatunji Alausa
Masana ilimi sun yi amanna cewa idan har aka kammala waɗannan ayyuka, za a samu sauƙi ƙwarai wajen rage ƙuncin da ɗaliban jami'o'i da kwalejoji ke fuskanta, musamman 'ya'yan talakawa da ke dogara da masaukin makaranta.

No comments