Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sabon salon da ta ɓallo da shi na yin amfani da bayanan sirri da leƙen asiri wajen yaƙar rashin tsaro, ya ...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a birnin Abuja, lokacin da yake tattaunawa da wakilan gidajen jaridun ƙasashen waje.
Ministan ya bayyana cewa a yanzu gwamnati ta canza sheka daga jiran sai ɓarawo ya kawo hari kafin a mayar da martani, zuwa ga yin amfani da bayanan sirri domin daƙile harin tun kafin ya auku. Ya ce an samu kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin Sojoji, ’Yan sanda, DSS da kuma hukumomin leƙen asiri na ƙasa.
A cewarsa, wannan haɗin gwiwar ce ta kai ga kamo shahararren kwamandan ƙungiyar ISWAP, Mahmoud, da babban jami’insa, waɗanda ma hukumomin ƙasashen waje irin su Amurka ke nema ido rufe.
Idris ya buga misali da hanyar mota da ta jirgin ƙasa ta Abuja zuwa Kaduna, wadda a baya take matsayin sahun gaba a wuraren da ake garkuwa da mutane.
Ya ce: “Ina gaya muku, ni kaina jiya na dawo daga Kaduna ta wannan hanyar. A baya, ba wanda zai bi ta ba tare da ya yi tambaya ba, amma yanzu hakan ta kau. Hanyar ta zama lafiya sakamakon tura dakaru na musamman da kuma haɗin gwiwar jami'an tsaro."
Game da batun kafa ’yan sandan jihohi, Ministan ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu da Majalisar Ƙasa sun riga sun fara shirin yi wa kundin tsarin mulki garambawul. Ya ce ana sa ran kammala komai nan da ƙarshen shekarar 2026 bayan an tuntuɓi masu ruwa da tsaki a faɗin Nijeriya.
Ya bayyana cewa an samar da matakan kariya a cikin dokar domin tabbatar da cewa ba a yi amfani da ’yan sandan jihohin wajen cin zarafin mutane ba.
Haka kuma, Ministan ya taɓo batun ikon ƙananan hukumomi, inda ya ce gwamnati ta fara tura musu da kuɗaɗen su kai-tsaye daga babban bankin ƙasa (CBN) kamar yadda Kotun Ƙoli ta bayar da umarni. Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da tsaro a matakin farko na rayuwar talakawa.
A nasa jawabin, Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya buƙaci ’yan jaridun ƙasashen waje da su riƙa yin adalci a rahotanninsu. Ya soki yadda wasu ke saurin bayar da labarin hare-hare amma su yi gum da baki lokacin da sojoji suka yi nasarar kashe ’yan ta’adda.

No comments