Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Rantsar Da Dr. Muttaqha Darma Matsayin Ministan Gidaje

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane na Tarayya a ranar Juma...

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane na Tarayya a ranar Juma'a.

Rantsar da Dr. Darma, wanda ɗan asalin jihar Katsina ne, ya biyo bayan amincewa da takardar nadinsa da Majalisar Dattawa ta yi. Ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa wanda ya yi murabus kwanan nan.

A wani taƙaitaccen biki da aka gudanar a fadar mulki ta Villa, Shugaba Tinubu ya taya sabon ministan murna, inda ya bayyana cewa ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen neman ci gaba.

Shugaban ya yaba wa Dr. Darma inda ya ce: "Kuna da kwarewa da kyakkyawan tarihin aiki. A matsayinmu na shugabanni, muna buƙatar ƙwararru irin ku. Babu shakka kun taka rawar gani a duk inda kuka yi aiki a baya, don haka kun dace da wannan matsayi."

Wane ne Dr. Muttaqha Darma?
Dr. Darma babban masani ne kuma kwararren mai gudanarwa wanda ya yi karatun digiri na uku (PhD) a fannin harkar kasuwanci daga Jami'ar Liverpool, da kuma wani PhD din a fannin "Industrial Engineering" daga Amurka.

Tarihinsa na karatu da aiki ya haɗa da:
• Digiri na farko a fannin "Mechanical Engineering" daga Jami'ar Bayero ta Kano (BUK).
• Ya taba zama Sakataren Gudanarwa na Asusun Tallafawa Fasahar Man Fetur (PTDF) daga 2008 zuwa 2012.
• Ya riƙe muƙaman Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, da kuma Kwamishinan Matasa da Walwalar Jama'a a Jihar Katsina.
• Ya taba zama malami a Jami'ar Bayero ta Kano. 

Kafin wannan naɗe-naɗe, Dr. Darma shi ne Shugaban Cibiyar Bunƙasa Ɗan Adam ta Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Sabon ministan ya sha alwashin yin amfani da ƙwarewar sa domin tabbatar da cewa an samar wa 'yan Nijeriya gidaje masu rahusa da kuma inganta biranen ƙasar kamar yadda tsarin gwamnati mai ci ya tanada.

 

No comments