Daga Zubairu Lawal, Lafia Wasu Shugabannin ƙungiyar NURTW da suka tsoma kansu cikin rikicin uwar ƙungiyar ta Ƙasa Sun fuskanci hukuncin dak...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Wasu Shugabannin ƙungiyar NURTW da suka tsoma kansu cikin rikicin uwar ƙungiyar ta Ƙasa Sun fuskanci hukuncin dakatarwa daga Ofishin Shugaban ƙungiyar reshen Jihar Nasarawa.
Shugabannin da aka dakatar guda 6 Sun fito ne daga reshen ƙungiyar da ke Ƙaramar Hukumar Karu a tashar mota ta Sani Abacha Bus Taminus.
Da yake zantawa da Wakilin mu, Sakataren Ƙungiyar reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Adamu Idiris Abdullahi ya bayyana cewa, waɗanda aka dakatar sun tsoma kansu ne cikin rikicin uwar ƙungiyar da aka yi na batun Shugabancin da wasu ya'yan ƙungiyar da ke yankin Kudanci ke yi.
Ya ce sun shiga cikin tarzomar da aka yi a Ofishin ƙungiyar. Inda aka lalata abubuwan ci gaba na ƙungiyar, hakan ne ya sanya aka dakatar da su, Kuma ana bincike. "DUK Wanda aka samu da laifi za a hukunta shi, kuma Idan ba a same su da laifi ba, za su dawo bakin aikin su," ya ce.

No comments