Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TSAGAITA WUTA: Amurka Ta Amince Da Sharuɗɗan Da Iran Ta Gindaya Mata

Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ƙasar Amurka ta amince da sharuɗɗan tsagaita wuta da Tehran ta gindaya...




Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ƙasar Amurka ta amince da sharuɗɗan tsagaita wuta da Tehran ta gindaya, bayan abin da ta bayyana a matsayin mummunar kaye da Amurka ta fuskanta.

A cikin sanarwar da majalisar ta fitar, ta ce wannan matsaya na Amurka zai zama tubalin fara tattaunawa a nan gaba tsakanin bangarorin biyu, inda aka jaddada cewa sharuɗɗan da Iran ta shimfiɗa sun zama tushen ci gaba da tattaunawar diflomasiyya.

Majalisar ta bayyana manyan sharuɗɗan da aka amince da su kamar haka:

Na farko, Amurka ta amince da ƙudurin kaucewa duk wani hari ko barazana ga Iran, wanda ke nuni da sabon salo na hulɗa da zai mayar da hankali kan zaman lafiya maimakon rikici.

Na biyu, an tabbatar da cewa Iran za ta ci gaba da riƙe cikakken iko a kan mashigar ruwan Hormuz, wacce ke da muhimmanci matuƙa ga safarar mai a duniya.

Na uku, an amince da haƙƙin Iran na ci gaba da tace sinadarin uranium, matakin da ya daɗe yana haifar da cece-kuce a tsakanin ƙasashen duniya.

Na huɗu, sanarwar ta ce za a ɗage dukkan takunkuman tattalin arziki—na farko da na biyu—da aka ƙaƙaba wa Iran, domin bai wa tattalin arzikinta damar farfaɗowa.

Na biyar, an cimma matsaya kan soke dukkan ƙudurorin da United Nations Security Council da kuma kwamitin gwamnonin International Atomic Energy Agency suka ƙaƙaba a baya kan Iran.

Na shida, Amurka ta amince da biyan diyya ga Iran bisa asarar da ta yi sakamakon rikice-rikicen da suka gabata.

Na bakwai, sanarwar ta ce za a janye dukkan sojojin Amurka daga yankin Gabas ta Tsakiya, matakin da ake ganin zai rage tashin hankali a yankin.

Na takwas kuma na ƙarshe, an jaddada cewa dukkan hare-hare da rikice-rikice a fannoni daban-daban za su tsaya cak, a wani ynƙuri na samar da cikakken zaman lafiya.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na duniya na ganin wannan sanarwa a matsayin babbar alama ta sauyin yanayi a dangantakar Amurka da Iran, duk da cewa ana sa ran ƙarin tattaunawa da tantancewa za su biyo baya domin tabbatar da dorewar yarjejeniyar.

No comments