Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NAZARI: Yadda CBN Ke Ta Ƙoƙarin Daƙile Malejin Hauhawar Farashi Zuwa Ƙasa Da Kashi 10 Bisa 100

Daga Ashafa Murnai Barkiya Ƙudurin Nijeriya na daƙile hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100, yana nan daram duk da ɗan ƙarin da ak...

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Ƙudurin Nijeriya na daƙile hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100, yana nan daram duk da ɗan ƙarin da aka samu a alƙaluman watan Maris sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da sauran ƙalubalen tattalin arziki. 

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa Nijeriya za ta cimma mafi ƙanƙantar malejin hauhawar farashin da bai kai ma'aunin kashi 10 bisa ba, duk da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tashi zuwa kashi 15.38 cikin ɗari a watan Maris daga kashi 15.06 cikin ɗari a watan Fabrairu.

Hasashen ci gaban tattalin arziki da juriyar fuskantar girgizar tattalin arzikin duniya duk da ƙalubale na daga cikin sakamakon gyaran fuskar harkokin kuɗi da CBN ke jagoranta domin gina tattalin arziki mai ƙarfi.

A duniya baki ɗaya, an amince cewa hauhawar farashi na a sahun gaba wajen haifar da cikas ga ci gaba, sannan kuma jibadau ne, wato babban nauyi ga talakawa.

A Nijeriya kuwa, gyare-gyaren tattalin arziki na sama da shekaru biyu da CBN ke yi, sun ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, tare da shirya shi don jurewa girgiza da kuma bunƙasa duk da matsaloli iri-iri.

Yanzu Nijeriya tana cikin matsayi mai kyau wajen jure wa matsin tattalin arziki daga ƙasashen waje. Akwai fahimta da yabo mai ƙarfi cewa gyare-gyaren tattalin arzikin Nijeriya sun ƙara wa masu zuba jari na gida da na ƙasashen waje ƙwarin gwiwa.

Da yake jawabi yayin taron Bankin Bada Lamuni na Duniya, 'International Monetary Fund' (IMF) da Bankin Duniya a Amurka, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo ɗan tashin hauhawar farashi a watan Maris, ya kasance cikin wani ɗan lokaci mai iyaka.

Ya ce ikon tattalin arzikin Nijeriya wajen shawo kan matsalolin da rikicin ya haifar yana nuna kyakkyawan sakamakon gyare-gyare, ciki har da daidaituwar canjin kuɗi, ƙaruwar adadin ajiyar kuɗaɗen waje da kuma ingantaccen tsarin manufofin kuɗi.

Cardoso ya ce: “Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara ƙarfin tattalin arziki da kuma ci gaba da tafiya kan manufar mu ta rage hauhawar farashi zuwa matakin da tsananin sa bai kai kashi 10 bisa ɗari ba. Duk da duk abin da ke faruwa, za mu ci gaba da bin wannan hanya.”

Tuni dai Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ƙarƙashin jagorancin Babban Mai Kididdiga na Ƙasa, Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta kai kashi 15.38 cikin ɗari a watan Maris 2026 daga kashi 15.06 cikin ɗari a watan Fabrairu.

Wannan shi ne karo na farko cikin watanni 12 da aka samu ƙaruwa tun bayan da hauhawar farashi ta fara raguwa tun daga watan Afrilu 2025.

NBS ta ce hauhawar farashin a watan Maris 2026 ya kai kashi 15.38 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 27.35 cikin ɗari a watan Maris 2025.

Hukumar ta bayyana cewa hauhawar farashin ya ƙaru da ɗigo 0.32 idan aka kwatanta da watan Fabrairu 2026.

A wata-wata kuwa, hauhawar farashi a watan Maris 2026 ta kai kashi 4.18 cikin ɗari, wanda ya fi na watan Fabrairu 2026 da kashi 2.17.

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya kuma umarci masu kula da harkokin tattalin arziki su samar da manufofi da za su rage tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya ga talakawa.

Matakan CBN Don Rage Hauhawar Farashi:

CBN ya ce gyare-gyaren tsarin tattalin arziki sun fara yin tasiri a faɗin tattalin arziki, suna taimakawa wajen daidaita darajar naira da rage adadin ladar kuɗin rance yayin da hauhawar farashi ke sauka a hankali.

A cewar CBN, matakan manufofin kuɗi da aka ɗauka wani ɓangare ne na dabarar dawo da daidaiton tattalin arziki bayan shekaru na matsin tattalin arziki da ƙalubalen kuɗaɗen gwamnati.

Waɗannan ci gaba suna nuna jajircewar shugabancin bankin wajen dawo da kwanciyar hankali a tsarin kuɗi, yayin da rage kuɗin ruwa na rance ke zama ɗaya daga cikin sakamakon manufofin CBN.

CBN ya ce haɗa manufofin kuɗi da na kasafin gwamnati abu ne mai muhimmanci musamman a lokacin da fasahar zamani da harkokin kuɗi ta dijital ke canza tsarin kuɗi.

A ƙarƙashin jagorancin Cardoso, CBN na ƙoƙarin samar da hanyoyi daban-daban na samun dala domin ƙara shigar kuɗin waje, samar da damar samun dala ga masana’antu da masu amfani na buƙatun yau da kullum na dole.

CBN ya kuma hanyoyin shigar dala a cikin ƙasa, ta hanyoyin inganta adadin kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida, zuwa bayar da lasisi ga sababbin kamfanonin canja kuɗi na duniya (IMTOs), da aiwatar da tsarin kasuwar canjin kuɗi tsakanin mai siya da mai sayarwa.

Wannan ya taimaka wajen ƙara yawan adadin ajiyar kuɗin waje da kuma tabbatar da nagartar naira.

Saboda muhimmancin shigar kuɗin waje wajen tabbatar da daidaiton manufofin kuɗi da kasafi, CBN na ƙara ƙoƙarin jawo ƙarin kuɗin shiga ga tattalin arziki.

Kuɗin da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida, wanda ake kiyasta ya kai dala biliyan 23 a shekara, na ci gaba da zama muhimmiyar hanyar samun kuɗin waje.

Cardoso ya ce Nijeriya na samun kusan dala miliyan 600 a kowane wata daga waɗannan kuɗaɗen.

Ya ce raguwar hauhawar farashi, kwanciyar hankali a kasuwar canjin kuɗi da ƙaruwar ajiya sun ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa.

IMF ta yaba wa manufofin tattalin arzikin Nijeriya, yana mai cewa gyare-gyaren cikin gida sun fara nuna sakamako.
 

No comments