Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta kare rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan, tana mai cewa Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin wani taron manema labarai kan halin tsaro a Filato, sakamakon harin da aka kai Angwan Rukuba a Jos ta Arewa.
Ya ce: “Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga masu aikata laifuka ba. Za mu kare jama’ar mu, kuma za mu yi nasara.”
Ya ƙara da cewa bai kamata ’yan Nijeriya su bari masu aikata laifuka su raba kan al’umma ba, yana mai jaddada cewa haɗin kan ƙasar nan yana nan daram, kuma dole ne a haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar nan.
Ministan ya nuna alhini kan harin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma gwamnati da al’ummar Jihar Filato.
Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda aka tura sojoji ƙarƙashin 'Operation Enduring Peace' domin shawo kan lamarin.
A cewar sa, matakan gaggawar da aka ɗauka sun taimaka wajen daƙile yaɗuwar rikicin da kuma hana ƙara tsananta al’amarin.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan da ke cikin haɗari ta hanyar amfani da bayanan sirri, ƙara yawan jami’ai, da kuma sintiri na haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ’yan sanda.
Idris ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya gana da manyan shugabannin tsaro domin duba halin da ake ciki da kuma ɗaukar ƙarin matakai masu tsauri.
Haka kuma ya ce an gayyaci Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, domin ƙarin tattaunawa da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ministan ya yaba da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na sanya dokar hana fita na sa’o’i 48 a Jos ta Arewa domin daidaita al’amura da tallafa wa ayyukan tsaro.
Duk da bayyana harin a matsayin abin takaici, Idris ya ce hakan ba yana nufin gazawar tsaro gaba ɗaya ba ne, illa dai aikata laifi a yankin da ke fama da rikice-rikice, yana mai tabbatar da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata laifin.
“Ba za a samu mafaka ga masu aikata laifuka a ko’ina cikin Nijeriya ba,” inji shi.
Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su tare da bin doka, yana mai gargaɗi kan yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, wanda ka iya ƙara ta’azzara rikici.
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa tattara bayanan sirri, shirye-shiryen tsaro da kuma haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.

No comments