Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MATAKAN DAƘILE 'YAN YAHOO-YAHOO: CBN Ya Gindaya Wa Bankuna Wa’adin Cika Tsauraran Matakan Tsaron Hada-hada A Yanar Gizo

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna su kammala tsare-tsaren tantance ƙa'idojin tsaron hada-hadar yanar gizo cikin makonni uk...

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna su kammala tsare-tsaren tantance ƙa'idojin tsaron hada-hadar yanar gizo cikin makonni uku, a wani yunkuri na ƙarfafa juriyar tsarin kuɗi na ƙasa.

A cikin wata wasiƙa da aka fitar a ranar 30 ga Maris, 2026, wadda aka wallafa a shafin CBN na yanar gizo ranar Talata, babban bankin ya jaddada cewa: “Dole ne cibiyoyi su gabatar da cikakken rahoton 'CSAT' cikin wa’adin da aka tsara kamar haka: (i) Makonni uku ga Bankunan Ajiyar Kuɗi; (ii) Makonni biyar ga sauran cibiyoyin da ake kula da su.”

Umarnin, wanda aka aika ga bankuna da wasu zaɓaɓɓun cibiyoyin kuɗi da masu samar da ayyukan biyan kuɗi, ya gabatar da wata na’ura mai suna 'Cybersecurity Self-Assessment Tool' (CSAT) domin tantance irin haɗarin tsaron yanar gizo da cibiyoyin ke fuskanta.

CBN ta bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da ikon da doka ta ba shi a ƙarƙashin dokar 'Banks and Other Financial Institutions Act 2020' (BOFIA), tare da ƙudurin sa na inganta matakan tsaron yanar gizo a fannin kuɗi.

“A ƙoƙarin sa, CBN na cika nauyin da doka ta ɗora masa ƙarƙashin dokar BOFIA 2020, kuma bisa ƙudurin ƙarfafa juriyar tsaron yanar gizo a duk fannin kuɗi, yana sanar da dukkan Bankunan Ajiyar Kuɗi, Bankunan Sabis na Biyan Kuɗi, Bankunan Microfinance, Masu Samar da Ayyukan Biyan Kuɗi, Kamfanonin Kuɗi, da Cibiyoyin Bada Lamuni na Raya Ƙasa cewa an ƙaddamar da 'CSAT,” inji wasiƙar.

An tsara 'CSAT' ne a matsayin wata hanya ta sa-ido domin samar da cikakken bayani game da matsayin tsaron yanar gizo na cibiyoyin kuɗi. CBN ya ƙara da cewa na’urar za ta duba muhimman fannoni kamar:Tsarin shugabanci, manufofin kula da haɗari tsarin fasaha, haɗarin ɓangarorin waje, shirye-shiryen tunkarar hare-haren yanar gizo
da kuma juriyar aiki gaba ɗaya.

“CSAT wani tsari ne na sa-ido da aka tsara domin tattara cikakken bayani kan matsayin tsaron yanar gizo na cibiyoyin da ake kula da su,” inji CBN.

Ya ƙara da cewa bayanan da za a samu daga wannan aikin za su taimaka wajen inganta tsarin sa-ido da kuma ƙarfafa ikon sa-ido kan barazanar tsaron yanar gizo a tsarin kuɗin Najeriya.

Domin tabbatar da bin doka, CBN ya ce dukkan cibiyoyin da abin ya shafa dole ne su cika tare da gabatar da rahoton ta wata kafar yanar gizo ta musamman, inda za a aika da bayanan shiga, wat 'access credentials' ga jami’an tsaron bayanai da sauran masu ruwa da tsaki.

“Duk rahotanni dole ne su kasance cikakku tare da duk wasu takardun shaida masu dacewa,” inji sanarwar. Sannan kuma bayanan dole ne su nuna matsayin cibiyoyi kamar yadda suke a ranar 31 ga Disamba, 2025.

CBN ya kuma yi gargadi kan bayar da bayanan ƙarya ko marasa cika, yana mai cewa za a ɗauki matakin hukunci kan duk wanda ya karya doka.

“Ana tunatar da cibiyoyin da ake sa ido a kansu cewa duk bayanan da za su gabatar dole ne su kasance sahihai, cikakku, kuma masu tabbaci. Bayar da bayanan ƙarya, yaudara, ko marasa daidaito laifi ne na dokoki kuma zai jawo hukunci,” cewar wasiƙar.

Haka kuma, CBN bayyana shirin tantance rahotannin ta hanyar duba su daga nesa da kuma ganawa da cibiyoyi domin tabbatar da sahihancin bayanan.

Wannan umarni wanda ya fara aiki nan take, na nuna ƙara tsaurara matakan sa-ido kan haɗarin tsaron yanar gizo a fannin banki, musamman a lokacin da ake samun karuwar mu’amalolin zamani ta hanyoyin yanar gizo, wato dijital da kuma barazanar hare-haren yanar gizo.
 

No comments