• Dole A Kamo Wadanda Suka Kashe Mutane a Angwan Rukuba Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hare-...
• Dole A Kamo Wadanda Suka Kashe Mutane a Angwan Rukuba
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hare-haren rashin imani da wasu ‘yan bindiga suka kai a gundumar Angwan Rukuba da ke Jos, Jihar Filato, da kuma ƙauyen Kahir da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.
Shugaban ya bayyana waɗannan hare-hare, waɗanda suka haɗa da kisan jama’a a Jos da kuma garkuwa da baƙi ’yan bikin aure a Kaduna, a matsayin babban ƙalubale ga haɗin kan Nijeriya. Ya kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa ba za a zura ido waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin su sha da daɗi ba.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa kan fannin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana maharan a matsayin azzalamai kuma matsorata.
> "Duk wanda zai fake da duhun dare ya kashe mutanen da ba su da kariya kamar yadda aka yi a Jos da kauyen Kahir, to matsoraci ne marar tausayi. Manufar wadannan maharan ita ce su haifar da ramuwar gayya domin jini ya ci gaba da kwarara," in ji Shugaban.
Shugaba Tinubu ya ba wa jami’an tsaro umarnin su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata laifin da kuma wadanda ke yada labaran karya da nufin ruruta wutar rikici. Haka kuma, ya ja kunnen wasu bangarorin kafafen yada labarai da ke kokarin danganta hare-haren da batun addini.
Babban matakin da Shugaban ya ɗauka sun hada da:
* Kiran Jami'an Tsaro: Ya buƙaci jami'an tsaro su riƙa amfani da bayanan sirri don dakile hare-hare kafin su auku.
* Ceton Waɗanda Aka Sace: Ya ba da umarnin gaggauta ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Kahir.
* Kayayyakin Aiki: Ya bƙyyana cewa gwamnati na kan hanyar sayo manyan makaman zamani don bin sawun miyagun mutane a duk inda suke.
Shugaban ya jinjina wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa kokarinsu na shawo kan lamarin da kuma tallafawa ayyukan ceto.
Daga ƙarshe, ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalai da suka rasa rayukansu, sannan ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata, yana mai kira ga al’umma da su ba wa jami’an tsaro hadin kai don tabbatar da zaman lafiya.

No comments