Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Tallafa Wa Gidaje Miliyan 15 Ta Hanyar HoPE-CT – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kai tallafi ga gidaje masu rauni miliyan 15 a fa...

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kai tallafi ga gidaje masu rauni miliyan 15 a faɗin ƙasar nan ta hanyar Shirin Tallafin Kuɗi na Inganta Rayuwar Iyali (HoPE-CT).

Idris, wanda Daraktan Hulɗa da Jama’a a ma'aikatar, Dakta Suleiman Haruna, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin taron bayani kan aiwatar da shirin da kuma ganawa da manema labarai.

Ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen tallafin jama’a mafi tasiri, yana mai cewa ya riga ya kai ga sama da mutane miliyan 9.2 a sassa daban-daban na ƙasar nan.

A cewar sa, shirin ya haɗa da bayar da tallafin kuɗi na N50,000 ga gidaje miliyan 3.6 domin tallafa wa rayuwar su da kuma rage talauci.

Ya ce: “Shirin HoPE-CT na nufin dawo da kyakkyawar fata, faɗaɗa damarmaki da kuma shimfiɗa tubalin wadata mai haɗa kowa. Hakan na nuna cewa gwamnati tana kula da buƙatun jama’a, musamman marasa galihu.”

Ministan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su mayar da hankali kan tasirin da irin waɗannan shirye-shiryen suke yi ga rayuwar jama’a, ta hanyar bayar da sahihan rahotanni.

Ya ce: “A matsayin ku na masu bayar da labari, ya dace ku haskaka yadda waɗannan shirye-shirye suke canza rayuwar jama’a, ta hanyar nuna halin da suke ciki a baya da kuma yadda rayuwar su ta inganta, domin ƙarfafa kyakkyawar fata da amincewa da gwamnati.” 

Idris ya sake jaddada cewa Shirin Sabunta Fata yana daga cikin manyan manufofin gwamnatin yanzu, kuma ya yi kira ga ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai.

Ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen tallafin jama’a, ciki har da rancen kuɗi ba tare da jingina ba ga matasa da mata, shirin lamunin ɗalibai, da kuma shirye-shiryen koyar da sana’o’i domin ƙarfafa tattalin arziki.

Ministan ya ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi domin inganta harkar yaɗa bayanai da hulɗa da jama’a kan shirye-shiryen gwamnati.

A ƙarshe, ya ce: “Yayin da muke karɓar shawarwari tare da inganta aiwatar da shirye-shiryen mu, za mu ci gaba da sauraro da kuma aiwatar da abin da ya dace. Tare, za mu gina Nijeriya inda babu wanda za a bari a baya.”
 

No comments