Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CIKAR WA'ADIN ƘARFAFA JARI: Yadda Bankunan Nijeriya Suka Bazama Tara Naira Tiriliyan 4.6 A Ƙoƙarin Cika Sharuɗɗan CBN

Bankunan kasuwanci a Nijeriya sun shiga wani sabon mataki na gasa mai zafi, yayin da bankuna 33 da suka samu nasarar tara kusan naira tirili...


Bankunan kasuwanci a Nijeriya sun shiga wani sabon mataki na gasa mai zafi, yayin da bankuna 33 da suka samu nasarar tara kusan naira tiriliyan 4.6 a ƙarƙashin shirin ƙarfafawa da bunƙasa jari na Babban Bankin Najeriya (CBN), wanda wa'adin sa ke cika a ranar Talata, 31 ga Maris 2026.

Wannan ya haifar da abin da masana ke kira gasa tsakanin sassa don samun damar bayar da rance mai cike da samun tagomashi.

Bincike ya nuna cewa tara wannan jari, wanda aka samu ta hanyoyi daban-daban kamar haƙƙin sayen hannun jari (rights issue), sayar da hannun jari ga jama’a, saka hannun jari daga masu zaman kan su, da kuma haɗin gwiwa, ya ba bankunan damar cika wa’adin da hukuma ta gindaya, tare da ƙarfafa ƙididdigar adadin kuɗaɗen su da kuma ikon ɗaukar manyan ayyukan ba da rance.


Wa'adin Naira Bilyan 500 Mafi Karancin Jari: 

Bankunan ƙasa da ƙasa na ne aka ba wannan umarni da wa'adi, a ƙarƙashin sabon tsarin ƙarfafa jarin CBN ya gindaya. Bankunan kasuwanci masu lasisin aiki a ƙasashen waje dole ne su mallaki aƙalla naira biliyan 500 a matsayin jarin da aka biya, wanda ya ninka sau tara daga tsohon adadi na naira biliyan 50.

Duk da shakku da aka fara yi kan ko kasuwa za ta iya ɗaukar wannan nauyin, “Manyan Bankuna Bakwai” ba wai sun cika sharadin kawai ba ne, har ma wasu sun zarce adadin.

Access Holdings Plc, waso Access Bank ya zama na farko da ya kammala wannan aiki, inda ya tara naira biliyan 351.01 ta hanyar amfani da tsarin dijital na NGX. Wannan ya ɗaga jarin bankin zuwa naira biliyan 600, wanda ya zarce adadin da aka nema.

Zenith Bank Plc shi ma ya nuna ƙarfin sa, inda ya tara naira biliyan 289.44 ta hanyoyin haɗaka. Babbar Daraktar Access Bank, Dakta. Adaora Umeoji, ta bayyana cewa an yi wannan ne domin haɓaka girma da kuma faɗaɗa aiki zuwa yankunan kasashe rainon Faransa a Afirka ta hanyar reshen Paris. Jimillar jarin bankin yanzu ya kai naira biliyan 614.65.

Guaranty Trust Holding Company (GTCO) ya ƙara jarin GTBank zuwa naira biliyan 504 bayan tara naira biliyan 365.85. Haka kuma ya zama bankin farko a Afirka ta Yamma da ya yi rijista a kasuwannin hannun jari biyu—NGX da London Stock Exchange—inda ya samu dala miliyan 105 daga masu saka jari na ƙasa da ƙasa.

Fidelity Bank ma ya yi fice, inda ya tara naira biliyan 272.95, tare da yawan masu neman sayen hannun jarin da ya zarce kima sosai.
Sauran bankuna kamar UBA, FCMB, da First Bank su ma sun tabbatar da matsayin su, inda First Bank ke shirin kai jarin sa zuwa naira biliyan 748.


Ƙarfafuwar Bankunan Kasa da na Yanki:

A bangaren bankunan ƙasa da na yanki, labarin ya ta’allaka ne kan haɗewa da kuma tallafin kamfanoni.
Bankunan ƙasa, waɗanda ake buƙatar su jarin kowanen su ya kai naira biliyan 200, sun nuna ƙwazo sosai.
Stanbic IBTC Holdings ta cimma wannan buri bayan tara naira biliyan 181.4, tare da ƙarin masu sayen hannayen jari da ya kai kashi 21.9%.

Ga bankunan waje kamar Ecobank Nigeria, Standard Chartered da Citibank, sun samu damar cika sharadin ne ta hanyar tallafin kamfanonin su na waje. Misali, Ecobank ya samu dala miliyan 125 daga uwar kamfanin sukutum.

Babban abin lura a wannan rukuni shi ne haɗewar Providus Bank da Unity Bank, inda CBN ya bada tallafin naira biliyan 700 domin tabbatar da dorewar sabon bankin.

A gefe guda, Wema Bank ya kai sama da naira biliyan 200 bayan tara naira biliyan 150 ta hanyar  wasu hanyoyi daban-daban.

A rukunin bankunan yanki da na kasuwanci (merchant banks), inda ake buƙatar naira biliyan 50, bankuna kamar Nova Bank, Parallex Bank da Titan Bank sun cika sharadin. Haka kuma bankunan kasuwanci irin su Rand Merchant Bank, Coronation da FSDH sun daidaita jarin su.

Bangaren bankunan da ba sa karɓar kuɗin ruwa, an samu gagarumin ci gaba.
Jaiz Bank, wanda shi ne ya fara irin wannan tsarin a Nijeriya, yana kan gaba da jarin naira biliyan 47.9—fiye da sau biyu na abin da ake buƙata, wato naira biliyan 20.
Wannan ya samu ne bayan tara naira biliyan 10.04.

Sauran bankuna kamar Lotus Bank, Taj Bank, da The Alternative Bank duk sun cika sharadin, yayin da Summit Bank ya shiga a matsayin bankin yanki da jarin naira biliyan 15.3.
 

No comments