Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Canja Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Riƙe Kuɗi A Hannun 'Yan Ta'adda - Ado Dansudu

Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna  Wani Dattijo mai yin sharhi kan al'amuran yau da kullum, wanda ya ke kuma shi ne Shugaban ƙungiyar ...

Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna 

Wani Dattijo mai yin sharhi kan al'amuran yau da kullum, wanda ya ke kuma shi ne Shugaban ƙungiyar 'Arewa united consultative forum,' Alhaji Ado Shu'aibu Dansudu ya yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba Babban Bankin ƙasar nan umurni don canja tkardar Naira, inda ya bayyana cewa yin hakan zai kawo ƙarshen riƙe kuɗi da 'yan ta'adda ke yi a ƙasar nan.

Ado Dansudu ya yi wannan kira ne yayin zantawa da manema labarai a Kaduna cikin makon nan, inda ya jaddada cewa gaggauta canja l kalar kuɗin da Babban Bankin Nijeriya zai yi zai kawo ƙarshen riƙe kuɗaɗen da ke hannun 'yan ta'adda.  

Ya ce, "Idan aka ɗauki wannan mataki zai rage wa 'yan ta'addan ƙarfi. Domin sun karbi bilyoyin nairori a hannun 'yan Nijeriya, kuma kuɗi tsaba, kuɗin da bankuna ba sa amfana, 'yan kasuwa ba sa amfana. Don haka canja kuɗin ne kawai zai koma da su baya, kuma su san Gwamnati, Gwamnati ce."

Shugaban na 'yan Arewa Grassroots movement for Tinubu a Legas ya kuma ƙara da cewa a 1983 Gwamnati Buhari ta canja kalar naira. Wai saboda 'yan Siyasa sun saci kuɗi sun boye a gidajen su, sannan 2023 zuwa 2024. 

Gwamnati Buhari ta canja kuɗi wai saboda kada a sayi ƙuri'un Mutane da kuɗi. "Dan haka muna kira da babbar murya ga Gwamnatin tarayya da ta gaggauta canja kalar kuɗin Nijeriya, sannan a sa jami'an DSS da EFCC a kowanne Banki don sanya ido ga masu shiga da kuɗi," in ji shi.

Ya ƙara dabcewa, "Wannan zai taimaka gaya wajen shawo kan rashin tsaron da mu ke fama da shi. Idan suka ga duk abin da suka mallaka ya zama abin banza, wasu za su yi wa kansu ƙiyamar laili."
 

No comments