Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan CBN Ya Jaddada Muhimmancin Ƙarfafa Cibiyoyi Da Gyaran Jarin Bankuna Domin Bunƙasar Tattalin Arziki Mai Ɗorewa

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya jaddada buƙatar gina cibiyoyi masu ƙarfi da kuma kyawawan ginshiƙan harkokin...

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya jaddada buƙatar gina cibiyoyi masu ƙarfi da kuma kyawawan ginshiƙan harkokin kuɗi domin tabbatar da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa a Nijeriya.

Cardoso ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da lacca ta musamman ga tsofaffin ɗalibai a bikin Founders’ Day na Kwalejin St. Gregory’s da ke Legas, inda ya yi jawabi kan taken “Strong Foundations: From the Classroom to the Capital Base.”

Ya ce irin ƙimomin da ke gina ƙwararrun mutane kamar ladabi, gaskiya da ɗaukar nauyi su ne kuma ginshiƙai masu muhimmanci wajen gina cibiyoyi masu ƙarfi da kuma tattalin arziki mai ɗorewa.

A cewar sa, ba za a iya samun daidaiton tattalin arziki mai ɗorewa ta hanyar matakan gaggawa na ɗan lokaci kawai ba, sai ta hanyar manufofi masu tsari, cibiyoyi masu tsare gaskiya da kuma tsarin kuɗi mai juriya.

Cardoso ya bayyana cewa tsarin kuɗin Nijeriya ya fuskanci matsin lamba a shekarun baya-bayan nan, ciki har da sauye-sauyen farashin canjin kuɗi, hauhawar farashi da kuma wasu matsalolin tsarin tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa babban bankin ya aiwatar da gyare-gyare domin dawo da amincewa da kuma ƙarfafa tsarin kuɗin ƙasar.

Ya ce shirin ƙara jarin bankuna da aka ƙaddamar a shekarar 2024 an tsara shi ne domin tabbatar da cewa bankunan Nijeriya suna da isasshen jari da zai tallafa wa sauyin tattalin arziki tare da jure duk wata girgiza.

Ya ce: “Ya zuwa ranar 12 ga Maris, 2026, bankuna 33 sun samu nasarar tara ƙarin jari, yayin da bankuna 30 suka riga suka cika sabon mafi ƙarancin jarin da ake buƙata bisa ga nau’in lasisin su.

“Sauran cibiyoyin kuma suna cikin tsarin tantancewa na yau da kullum da CBN ke yi, bisa jadawalin bin ƙa’ida.”

Cardoso ya ƙara da cewa babban bankin ya dawo da tsarin manufofin kuɗi na gargajiya tare da rage tsoma baki na kuɗaɗen gwamnati da a baya suke kawo cikas ga yanayin tattalin arziki.

A cewar sa, waɗannan matakan sun taimaka wajen rage hauhawar farashi daga kusan kashi 34 a lokacin da ta kai ƙololuwar ta zuwa kusan kashi 15.

Ya ce gyare-gyaren da aka yi a kasuwar canjin kuɗi sun kuma kawar da tsarin farashin canji iri-iri tare da matuƙar rage gibin da ke tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage.

“Ribar kasuwar bayan fage ta ragu daga kusan kashi 50 a shekarar 2022 zuwa ƙasa da kashi biyu a matsakaici a shekarar 2025.”

Cardoso ya ƙara da cewa gyare-gyaren sun ƙara amincewar masu zuba jari, sun ƙara shigar jarin ƙasashen waje, tare da ƙarfafa ajiyar kuɗin waje na Nijeriya, wanda ya ce ya haura dala biliyan 50.

Ya jaddada cewa cibiyoyi masu ƙarfi su ne ginshiƙin jure wa matsalolin tattalin arziki, musamman a cikin yanayin duniya mai cike da rashin tabbas da ke tattare da rikice-rikicen siyasa da kuma sauye-sauyen kasuwar makamashi.

Ya ce: “Ginshiƙai masu ƙarfi ne ke tabbatar da ko tsarin zai iya jure girgiza. Wannan ka’ida tana aiki ga tattalin arziki, cibiyoyi da kuma ƙasashe.”

Cardoso, wanda shi ma tsohon ɗalibin Kwalejin St. Gregory’s ne, ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai a faɗin ƙasar nan da su tallafa wajen haɓaka shugabanci da kuma ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa.
 

No comments