Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

eKano Ta Samu Cibiyoyin Sauya Motoci Zuwa CNG Guda 41 Yayin Da Gwamnatin Tarayya Ke Ƙara Faɗaɗa Shirin

Gwamnatin Tarayya na ƙara ƙaimi wajen samar da hanyoyin makamashi masu sauƙi da aminci a fannin sufuri, inda aka riga aka samar da cibiyoyi ...


Gwamnatin Tarayya na ƙara ƙaimi wajen samar da hanyoyin makamashi masu sauƙi da aminci a fannin sufuri, inda aka riga aka samar da cibiyoyi 41 na sauya tsarin motoci zuwa amfani da iskar Compressed Natural Gas (CNG) a Jihar Kano.

Shirin, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samar, na da nufin rage tsadar sufuri da ƙarfafa tsaron makamashi ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta.

A wata ziyara da Babban Jami’in Shirin CNG na Ƙasa (PCNGi), Barr. Ismaeel Ahmad ya kai wurin ajiyar kayan sauya motoci da ke No. 12 Kakara Warehouse, kan titin Hadeja a Kano a ranar lahadi, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin kayan sauya mota 3,524 a cikin rumbun, waɗanda suka haɗa da tankuna masu girman lita 30, 65 da 75, kuma a shirye suke domin rabawa cibiyoyin da aka amince da su a faɗin jihar.

Ya ce cibiyoyin na da alhakin sauya motoci da adaidaita sahu daga man fetur zuwa amfani da CNG, matakin da ake sa ran zai rage kuɗin sufuri ga direbobi da fasinjoji.

A cewarsa, a yanzu cibiyoyi 41 na karɓar kayan daga rumbun domin hanzarta aikin sauya tsarin motoci tare da faɗaɗa damar cin gajiyar shirin.

Wasu daga cikin cibiyoyin sun haɗa da Trade Source Integrated Concept, PKM Global Resource Ltd, Drive Green, Safe Auto Gas Ltd, Dazle Integrated Service, Go CNG Now Ltd, S J Resource Limited, Arus CNG Conversion Center, Fonnd Motor Manufacturing, Enormous International Center, Danfyrt Autos Ltd, Afriks Ltd, AMK Integrated, ABG Oil & Gas, Green Africa Solutions, Amani Automobile Ltd, Ahad Projects Ltd, Pro-Prestige Ltd da Nuts and Bolt, da sauransu.

Shugaban PCNGi ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa shirin a faɗin ƙasar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage tasirin tsadar mai tare da inganta amfani da makamashi mai tsafta.

Ya ƙara da cewa yawaitar cibiyoyin a Kano na nuna yadda kamfanoni masu zaman kansu ke bada gudunmawa tare da karɓuwar shirin daga jama’a.

Masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri sun yabawa shirin, suna masu cewa lokaci ya yi da ya dace, musamman wajen rage kashe kuɗi da inganta rayuwar al’umma.

Ana sa ran wannan faɗaɗawar zai ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci ta hanyar rage kuɗin jigilar kaya da fasinjoji, tare da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da haɓaka tattalin arzikin jihar Kano baki ɗaya.







 

No comments