Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada aniyarsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, yana mai tabbatar da cew...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada aniyarsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta bari matsalar tsaro ta dakatar da ƙoƙarin tallafa wa talakawa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a birnin Lagos yayin da ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da gwamnoni 23 domin bikin Eid al-Fitr.
A cewarsa, gwamnatinsa na ƙara ƙoƙari wajen haɗa kai da ƙasashen duniya domin samun kayan aiki da fasahohin zamani na tsaro. Ya ce har ma ya tattauna da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, kan batun haɗin gwiwa a fannin tsaro.
> “Rashin tsaro abokin gaba ne ga ci gaba da walwala. Za mu tabbatar da cewa mun shawo kansa domin al’umma su ci moriyar zaman lafiya,” in ji Shugaban.
Shugaban ya kuma bayyana cewa ziyarar da ya kai Birtaniya ta mayar da hankali kan samar da tallafin tsaro da kayan aiki, inda ya gana da Firayim Minista Keir Starmer, tare da ganawa da Sarki King Charles III.
Shugaba Tinubu ya gargadi gwamnoni da su shirya yadda za su rage radadin hauhawar farashi da ka iya biyo bayan rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman a bangaren man fetur da sufuri.
"Ya zama wajibi a ƙara tallafawa marasa ƙarfi, a samar da manufofi da za su rage wahalar rayuwa, a kuma haɗa kai wajen kawar da zaluncin ‘yan ta’adda” inji shi
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya gode wa Shugaban bisa manufofin “Renewed Hope Agenda” da kuma nasarar ziyarar da ya kai ƙasar Birtaniya.
Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan batun kafa ‘yan sandan jihohi, inda NGF za ta kai shawarwarinta gaban Majalisar Tarayya.
Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnoni su ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma, yana mai jaddada cewa haɗin kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya shi ne mafita ga matsalolin ƙasar.

No comments