Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ƘARFAFA TSARO: Nijeriya Ta Ƙara Inganta Hulɗa Da Tarayyar Turai Bayan Ganawar Shugaba Tinubu Da Babbar Jami'ar EU

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da babbar jami’ar tarayyar turai (EU) mai kula da harkokin waje da tsaro, Kaja Kallas, a wani muhimmin tar...


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da babbar jami’ar tarayyar turai (EU) mai kula da harkokin waje da tsaro, Kaja Kallas, a wani muhimmin taro da aka gudanar a gidansa da ke jihar Legas.

A yayin ganawar, Shugaban Ƙasa tare da Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, sun tattauna kan hanyoyin ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Tarayyar Turai, musamman a fannonin tsaro, musayar bayanan sirri, da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ziyarar ta Kaja Kallas na nuni da yadda hulɗar Najeriya da Tarayyar Turai ke ƙara ƙarfi, musamman wajen haɗa kai don yaƙi da ta’addanci, inganta tsaron yanar gizo (cybersecurity), da kuma dakile laifukan ƙetare iyakoki.

Hakazalika, an jaddada muhimmiyar rawar da Nuhu Ribadu ke takawa wajen tsara manufofin tsaro na ƙasa da kuma jagorantar haɗin gwiwa da ƙasashen waje domin tinkarar barazanar tsaro.

Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ƙoƙarin haɗa kai da ƙasashen duniya domin magance matsalolin tsaro da ke ƙara tasowa, tare da ƙarfafa alaƙa da Tarayyar Turai
 

No comments