Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NEJA: ’Yan ta’adda Sun Ƙona Coci Da Ofishin ’Yan Sanda A Agwara

Wasu ’yan ta’adda da ake zargin ’yan bindiga ne sun sake kai wani mummunan hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja, inda s...




Wasu ’yan ta’adda da ake zargin ’yan bindiga ne sun sake kai wani mummunan hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja, inda suka ƙona ofishin ’yan sanda da kuma wata coci tare da sace mutane da dama, ciki har da uwa mai shayarwa da ’ya’yanta huɗu.

Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, inda maharan suka shiga ƙauyukan suna harbe-harbe tare da tada zaune tsaye.

An ce sun kuma kashe wata tsohuwa a qauyen Kabe kafin su kwashe kayan abinci masu yawa daga gidajen jama’a.

Majiyoyi sun bayyana cewa cocin da aka ƙona mallakin United Missionary Church of Africa (UMCA) ce, lamarin da ya kara jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun bar yankin ne da misalin ƙarfe shida na safe, inda suka nufi wani qauye mai suna Sokonbara, wanda ke kusa da Kabe, inda aka kuma kai hari.

Daga cikin wadanda aka sace har da shugaban makarantar firamare ta yankin, Malam Ahmed Burade, wanda tsohon shugaban kungiyar Malaman Makarantu ta Nijeriya (NUT) ne a yankin. Sai dai an ruwaito cewa ya samu nasarar tserewa yayin musayar wuta tsakanin maharan da ’yan sa-kai.

Duk da haka, matarsa mai juna biyu wadda ke shayarwa tare da ’ya’yansu huɗu na daga cikin wadanda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da harin ba.

Jihar Neja da makwabciyarta Kaduna na ci gaba da fuskantar yawaitar hare-haren ’yan bindiga a ’yan shekarun nan, inda ake kai farmaki kan ƙauyuka, cibiyoyin ibada da makarantu tare da kashe mutane da sace wasu domin neman kudin fansa.

Al’ummar yankunan da lamarin ya shafa na ci gaba da kira ga gwamnatocin tarayya da ta jiha da su kara ɗaukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

No comments