Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar ɗaukaka ƙara da Jami’ar Ribas (RSU) ta shigar, lamarin da ya kawo ƙarshen taƙaddamar da ta fara tun shekarar...
Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar ɗaukaka ƙara da Jami’ar Ribas (RSU) ta shigar, lamarin da ya kawo ƙarshen taƙaddamar da ta fara tun shekarar 2012 kan ’yancin ɗalibai Musulmi na gudanar da sallah da kuma kafa wurin ibada a harabar jami’ar da ke Nkpolu Oroworukwo.
Hukuncin da kotun ta yanke baki ɗaya ya tabbatar da hukuncin kotunan baya, wanda ya amince da ’yancin daliban na yin ibada cikin ’yanci tare da ware musu fili a harabar makaranta domin wannan manufa.
Shari’ar ta samo asali ne a 2012 lokacin da wasu ɗalibai Musulmi suka zargi mahukuntan jami’ar da hana su gudanar da sallah da kuma gina wuraren da suka shafi ibadar Musulunci. A cikin Shari’a mai lamba FHC/PH/CS/150/2012 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal, masu ƙara ƙarƙashin jagorancin Umaru Wazuru da wasu 98, sun kalubalanci matakin mataimakin shugaban jami’ar na wancan lokaci da kuma Babban Lauyan Jihar Rivers.
Ɗaliban, ta hannun lauyoyinsu daga kamfanin lauyoyi na Oloriegbe & Co., sun nemi kotu ta bayyana cewa matakan da jami’ar ta ɗauka sun saɓa wa kundin tsarin mulki kuma nuna wariya ne. Sun kuma roƙi kotu ta umarci jami’ar ta ware musu fili domin ibada, kamar yadda ake da wuraren ibada na Kiristoci a harabar makarantar.
A hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 19 ga Fabrairu, 2013, ta amince da bukatar daliban, tana mai cewa hana su kafa wurin ibada alhali akwai coci-coci a harabar makarantar ya saɓa wa ’yancin tunani, lamiri da addini da kundin tsarin mulki ya tanada. Kotun ta kuma yi watsi da hujjar jami’ar cewa masallaci bai cikin tsarin farko na ginin jami’ar, tana mai cewa wannan hujja ba ta dace da tanadin kundin tsarin mulki ba.
Jami’ar ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Fatakwal, amma a ranar 31 ga Maris, 2017, kotun ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya, tana mai tabbatar da hukuncin kotun tarayya.
Daga bisani an sake ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a shari’a mai lamba SC/055/2018, duk da cewa an nuna cewa an shigar da ita ne bayan wa’adin da doka ta tanada. A ranar 10 ga Fabrairu, 2026, Kotun Ƙoli ta saurari ƙarar tare da yin watsi da ita baki ɗaya, wanda hakan ya kawo ƙarshen shari’ar.
Da wannan hukunci, dukkanin hukunce-hukuncen kotunan baya da suka amince da ’yancin daliban Musulmi na yin ibada a cikin jami’ar tare da ware musu wurin da ya dace sun kasance masu ɗaurewa ga ɓangarorin da abin ya shafa.
A tsarin shari’ar Najeriya, hukuncin Kotun Ƙoli shi ne na ƙarshe kuma wajibi ne dukkan hukumomi da mutane su bi shi. Masana shari’a sun bayyana cewa rashin bin umarnin kotu na iya jawo tuhumar raina kotu, wanda zai iya kai ga hukunci ciki har da ɗauri a gidan yari.

No comments