Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

GOBARAR SINGER: Shugaban Ƙasa Ya Jajanta Wa ‘Yan Kasuwar Kano, Ya Ba da Umarnin Bincike

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa ‘yan kasuwa da al’ummar Jihar Kano sakamakon gobarar da ta tashi a Kasuwar Singer a ƙarshen ...

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa ‘yan kasuwa da al’ummar Jihar Kano sakamakon gobarar da ta tashi a Kasuwar Singer a ƙarshen makon nan. 

Gobarar, wadda ta fara da yammacin ranar Asabar, ta ci gaba da ƙonewa har zuwa safiyar Lahadi, inda ta haddasa mummunar asara musamman a sashen sayar da kayan abinci na kasuwar.

Shugaban Ƙasar, wanda tun da fari ya tuntubi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin samun cikakken rahoton halin da ake ciki, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuƙa.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin yawaitar gobarar kasuwanni, lamarin da ke jefa ‘yan kasuwa cikin halin kunci akai-akai.

No comments